Главная / Архив новостей
Архив новостей

В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.

Sojojin Sudan Sun Karya Ƙawanyar RSF a Dilling

Sun buɗe hanya bayan gagarumin farmaki a Kudancin Kordofan Rundunar sojin Sudan ta sanar da karya ƙawanyar da mayaƙan RSF suka shafe sama da shekara ɗaya da rabi suna yi wa birnin Dilling a kudancin ƙasar, bayan kaddamar da gagarumin farmakin soji da ya buɗe hanyar shiga birnin tare da jefa RSF c...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Обновлено 13.08.2026, 05:26:20
Sojojin Sudan Sun Karya Ƙawanyar RSF a Dilling
Кратко

Sun buɗe hanya bayan gagarumin farmaki a Kudancin Kordofan Rundunar sojin Sudan ta sanar da karya ƙawanyar da mayaƙan RSF suka shafe sama da shekara ɗaya da rabi suna yi wa birnin Dilling a kudancin ƙasar, bayan kaddamar da gagarumin farmakin soji da ya buɗe hanyar shiga birnin tare da jefa RSF c...

Sun buɗe hanya bayan gagarumin farmaki a Kudancin Kordofan Rundunar sojin Sudan ta sanar da karya ƙawanyar da mayaƙan RSF suka shafe sama da shekara ɗaya da rabi suna yi wa birnin Dilling a kudancin ƙasar, bayan kaddamar da gagarumin farmakin soji da ya buɗe hanyar shiga birnin tare da jefa RSF cikin mummunar ɓarna. TRT Hausa Sojojin sun ce za su ci gaba da yaƙi da RSF har sai an maido da zaman lafiya a faɗin Sudan, inda wannan nasara ke ƙara ƙarfafa matsayinsu a yankunan arewa da kudu da ke kan hanyar zuwa Dilling a jihar Kudancin Kordofan. TRT Hausa Rahotanni da bidiyoyi a kafafen sada zumunta sun nuna sojojin Sudan suna murna a cikin Dilling, lamarin da ke zuwa a daidai lokacin da RSF ke ƙoƙarin faɗaɗa hare-hare a yankin Kordofan bayan samun goyon baya daga wasu ƙungiyoyi da kuma ƙwace muhimman yankuna kamar Heglig. TRT Hausa