Home / News archive
News archive

This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.

Sojojin Sudan sun sha alwashin kwashe 'shekaru 100' suna yaƙi

Yaƙin Sudan ya raba miliyoyin mutane da muhallansu, inda dubbai suka yi gudun hijira zuwa ƙasashe maƙota, yayin da aka kashe dubbai. Shugaban mulkin sojin Sudan, Abdel Fattah al-Burhan, ya ce gwamnatinsa ba za ta shiga tattaunawar zaman lafiya da ake yi a Switzerland ba da rundunar kai ɗaukin gag...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Updated 13/08/2026, 05:26:20
Sojojin Sudan sun sha alwashin kwashe 'shekaru 100' suna yaƙi
At a glance

Yaƙin Sudan ya raba miliyoyin mutane da muhallansu, inda dubbai suka yi gudun hijira zuwa ƙasashe maƙota, yayin da aka kashe dubbai. Shugaban mulkin sojin Sudan, Abdel Fattah al-Burhan, ya ce gwamnatinsa ba za ta shiga tattaunawar zaman lafiya da ake yi a Switzerland ba da rundunar kai ɗaukin gag...

Yaƙin Sudan ya raba miliyoyin mutane da muhallansu, inda dubbai suka yi gudun hijira zuwa ƙasashe maƙota, yayin da aka kashe dubbai. Shugaban mulkin sojin Sudan, Abdel Fattah al-Burhan, ya ce gwamnatinsa ba za ta shiga tattaunawar zaman lafiya da ake yi a Switzerland ba da rundunar kai ɗaukin gaggawa ta ƙasar, yana mai cewa maimakon haka za su kwashe "shekara 100 suna yaƙi." "Ba za mu je Geneva ba... za mu kwashe shekaru 100 muna yaƙi," in ji Burhan, wanda dakarunsa suka kwashe watanni 16 suna fafatawa da mayaƙan rundunar kai ɗaukin gaggawa ta Rapid Support Forces. Ya bayyana haka ne ga manema labarai ranar Asabar a Port Sudan. Amurka ta buɗe wani shirin tattaunawa a Switzerland ranar 14 ga watan Agusta da zummar kawo ƙarshen bala'in da yaƙi ya jefa ƙasar ta Sudan. Wakilan RSF sun halarci wurin tattaunawar, sai dai gwamnatin Sudan ba ta amince da tsarinsa ba, kuma ba ta je wurin taron ba, ko da yake ta yi magana ta wayar tarho da masu shiga tsakani.