Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

Sojojin Sudan sun sha alwashin kwashe 'shekara 100' suna yaƙi

Yaƙin Sudan ya raba miliyoyin mutane da muhallansu, inda dubbai suka yi gudun hijira zuwa ƙasashe maƙota, yayin da aka kashe dubbai. Shugaban mulkin sojin Sudan, Abdel Fattah al-Burhan, ya ce gwamnatinsa ba za ta shiga tattaunawar zaman lafiya da ake yi a Switzerland ba da rundunar kai ɗaukin gag...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:20
Sojojin Sudan sun sha alwashin kwashe 'shekara 100' suna yaƙi
Kwa muhtasari

Yaƙin Sudan ya raba miliyoyin mutane da muhallansu, inda dubbai suka yi gudun hijira zuwa ƙasashe maƙota, yayin da aka kashe dubbai. Shugaban mulkin sojin Sudan, Abdel Fattah al-Burhan, ya ce gwamnatinsa ba za ta shiga tattaunawar zaman lafiya da ake yi a Switzerland ba da rundunar kai ɗaukin gag...

Yaƙin Sudan ya raba miliyoyin mutane da muhallansu, inda dubbai suka yi gudun hijira zuwa ƙasashe maƙota, yayin da aka kashe dubbai. Shugaban mulkin sojin Sudan, Abdel Fattah al-Burhan, ya ce gwamnatinsa ba za ta shiga tattaunawar zaman lafiya da ake yi a Switzerland ba da rundunar kai ɗaukin gaggawa ta ƙasar, yana mai cewa maimakon haka za su kwashe "shekara 100 suna yaƙi." "Ba za mu je Geneva ba... za mu kwashe shekara 100 muna yaƙi," in ji Burhan, wanda dakarunsa suka kwashe watanni 16 suna fafatawa da mayaƙan rundunar kai ɗaukin gaggawa ta Rapid Support Forces. Ya bayyana haka ne ga manema labarai ranar Asabar a Port Sudan. Amurka ta buɗe wani shirin tattaunawa a Switzerland ranar 14 ga watan Agusta da zummar kawo ƙarshen bala'in da yaƙi ya jefa ƙasar ta Sudan. Wakilan RSF sun halarci wurin tattaunawar, sai dai gwamnatin Sudan ba ta amince da tsarinsa ba, kuma ba ta je wurin taron ba, ko da yake ta yi magana ta wayar tarho da masu shiga tsakani. Gawarwakin mutane na rubewa a kan titunan babban birnin Sudan Saudiyya da Switzerland, da Tarayyar Afirka da Masar da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Majalisar Ɗinkin Duniya na cikin mahalarta taron wanda ke neman samar da dawwamammen zaman lafiya a Sudan. Sun kammala taron ranar Juma'a ba tare da cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta ba ko da yake an samu ci gaba game da shigar da kayan agaji ƙasar ta wasu muhimman hanyoyi. Yaƙin Sudan ya raba miliyoyin mutane da muhallansu, inda kimamin mutum miliyan 25 a faɗin ƙasar suke fama da bala'in yunwa.