Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

Sojojin Sudan sun sake ƙwace muhimman wurare daga dakarun RSF a El-Fasher

Wata sanarwa da rundunar sojin Sudan ta fitar ta ce dakarunta sun kai farmaki a wurare daban-daban da ke hannun mayaƙan RSF a El-Fasher inda suka sanya su yin asarar dakaru da kayayyakin aiki. Rundunar sojin Sudan ta ce ta ƙwato yankuna da dama da ke ƙarƙashin mayaƙan rundunar ko-ta-kwata ta Rapi...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:20
Sojojin Sudan sun sake ƙwace muhimman wurare daga dakarun RSF a El-Fasher
De un vistazo

Wata sanarwa da rundunar sojin Sudan ta fitar ta ce dakarunta sun kai farmaki a wurare daban-daban da ke hannun mayaƙan RSF a El-Fasher inda suka sanya su yin asarar dakaru da kayayyakin aiki. Rundunar sojin Sudan ta ce ta ƙwato yankuna da dama da ke ƙarƙashin mayaƙan rundunar ko-ta-kwata ta Rapi...

Wata sanarwa da rundunar sojin Sudan ta fitar ta ce dakarunta sun kai farmaki a wurare daban-daban da ke hannun mayaƙan RSF a El-Fasher inda suka sanya su yin asarar dakaru da kayayyakin aiki. Rundunar sojin Sudan ta ce ta ƙwato yankuna da dama da ke ƙarƙashin mayaƙan rundunar ko-ta-kwata ta Rapid Support Forces (RSF) a El-Fasher, babban birnin Jihar North Darfur da ke yammacin Sudan. Wata sanarwa da rundunar sojin Sudan ta fitar ta ce dakarunta sun kai farmaki a “wurare daban-daban” da ke hannun mayaƙan RSF a El-Fasher inda suka sanya su yin asarar dakaru da kayayyakin aiki. Kazalika rundunar sojin ta ce dakarun nata sun ƙwace motocin yaƙi da dama, ko da yake ba ta faɗi adadinsu ba, amma ta ƙara da cewa sun lalata motocin yaƙi shida, ciki har da motoci masu sulke. A cewar rundunar sojin, mayaƙan RSF sun ƙaddamar da hari a kudacin El-Fasher, amma sojojin gwamnati sun daƙile harin sannan suka haddasa musu asara mai yawa.