Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

Sojin ruwa sun kama masu ɓoyewa a jirgi a Legas

Ana zargin suna ƙoƙarin tserewa Turai ta haramtacciyar hanya Rundunar sojin ruwan Nijeriya ta kama mutum biyu da ake zargi da yunƙurin tserewa Turai ta hanyar ɓoyewa a cikin jirgin ruwa a tashar Legas. An gano su ne a cikin jirgin MV Seaspan Lahore yayin bincike na yau da kullum da jami’an tsaro...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:20
Sojin ruwa sun kama masu ɓoyewa a jirgi a Legas
De un vistazo

Ana zargin suna ƙoƙarin tserewa Turai ta haramtacciyar hanya Rundunar sojin ruwan Nijeriya ta kama mutum biyu da ake zargi da yunƙurin tserewa Turai ta hanyar ɓoyewa a cikin jirgin ruwa a tashar Legas. An gano su ne a cikin jirgin MV Seaspan Lahore yayin bincike na yau da kullum da jami’an tsaro...

Ana zargin suna ƙoƙarin tserewa Turai ta haramtacciyar hanya Rundunar sojin ruwan Nijeriya ta kama mutum biyu da ake zargi da yunƙurin tserewa Turai ta hanyar ɓoyewa a cikin jirgin ruwa a tashar Legas. An gano su ne a cikin jirgin MV Seaspan Lahore yayin bincike na yau da kullum da jami’an tsaro ke yi kafin tashin jirgin. Waɗanda aka kama sun haɗa da Abdullahi Yakubu da Omoniyi Afotona, waɗanda yanzu aka miƙa su ga Nigeria Immigration Service domin ci gaba da bincike da yiwuwar gurfanar da su a kotu. Kwamandan rundunar NNS BEECROFT, Commodore A. Adams-Aliyu, ya ce irin wannan hanya ta ɓoye a jirgi ta saɓa wa doka kuma tana da matuƙar haɗari. Ya kuma yi kira ga matasa su guji neman fita ƙasashen waje ta hanyoyin da ba su dace ba, tare da roƙon iyaye su wayar da kan ‘ya’yansu kan haɗarin hakan. Hukumomi sun jaddada cewa za su ci gaba da tsaurara matakan tsaro a tashoshin jiragen ruwa domin dakile irin waɗannan ayyuka. Tushen labari: Newstimehub