Home / News archive
News archive

This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.

Sojojin Nijeriya sun musanta kai hari kan masu maulidi a Kaduna

Rundunar Sojin Saman Nijeriya ta ce akwai bukatar a san cewa ba ita kadai ke amfani da jiragen yaki a Arewa Maso Yammacin Nijeriya ba. Rundunar sojin saman Nijeriya ta musanta wasu rahotanni da ke cewa jirgin yakinta ya kai hari kan masu bikin Maulidi a Kaduna. Tun da safiyar Litinin ne wasu daga...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Updated 13/08/2026, 05:26:20
Sojojin Nijeriya sun musanta kai hari kan masu maulidi a Kaduna
At a glance

Rundunar Sojin Saman Nijeriya ta ce akwai bukatar a san cewa ba ita kadai ke amfani da jiragen yaki a Arewa Maso Yammacin Nijeriya ba. Rundunar sojin saman Nijeriya ta musanta wasu rahotanni da ke cewa jirgin yakinta ya kai hari kan masu bikin Maulidi a Kaduna. Tun da safiyar Litinin ne wasu daga...

Rundunar Sojin Saman Nijeriya ta ce akwai bukatar a san cewa ba ita kadai ke amfani da jiragen yaki a Arewa Maso Yammacin Nijeriya ba. Rundunar sojin saman Nijeriya ta musanta wasu rahotanni da ke cewa jirgin yakinta ya kai hari kan masu bikin Maulidi a Kaduna. Tun da safiyar Litinin ne wasu daga cikin kafafen watsa labaran Nijeriya suka rinka ruwaito cewa jirgin sama wanda ake zargin na sojojin saman Nijeriya ne ya kai hari a Tudun Biri da ke Karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna. Lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:00 na dare a ranar Lahadi. “Labaran da ke yawo wanda ake zargin Rundunar Sojin Saman Nijeriya ta kai hari bisa kuskure kan farar hula a Kaduna ba gaskiya bane,” kamar yadda mai magana da yawun sojin saman Nijeriya Edward Gabkwet ya sanar. “Akwai bukatar a san cewa sojojin sama ba su kai wani samame a Kaduna a sa’o’i 24 da suka gabata ba. Haka kuma akwai bukatar a san cewa ba Rundunar Sojin Saman Nijeriya ce kadai ke amfani da jirage marasa matuka na yaki a Arewa Maso Yammacin Nijeriya ba,” in ji sanarwar.