Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

Sojojin Nijeriya sun lalata haramtattun matatun fetur

Ana yawan samun matatun mai da ake gudanar da su ba bisa ka'ida ba a Nijeriya, daya daga cikin manyan kasashe masu arzikin mai a nahiyar Afirka. Rundunar sojin saman Nijeriya ta ce ta lalata haramtattun matatun mai a yankin kudancin kasar, a wani harin da ta kai ta sama a jihar Ribas da ke kudanc...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:20
Sojojin Nijeriya sun lalata haramtattun matatun fetur
A taƙaice

Ana yawan samun matatun mai da ake gudanar da su ba bisa ka'ida ba a Nijeriya, daya daga cikin manyan kasashe masu arzikin mai a nahiyar Afirka. Rundunar sojin saman Nijeriya ta ce ta lalata haramtattun matatun mai a yankin kudancin kasar, a wani harin da ta kai ta sama a jihar Ribas da ke kudanc...

Ana yawan samun matatun mai da ake gudanar da su ba bisa ka'ida ba a Nijeriya, daya daga cikin manyan kasashe masu arzikin mai a nahiyar Afirka. Rundunar sojin saman Nijeriya ta ce ta lalata haramtattun matatun mai a yankin kudancin kasar, a wani harin da ta kai ta sama a jihar Ribas da ke kudancin kasar. Rundunar ta ce ta kai hare-haren ne a ranakun Litinin da Talata inda ta kara da cewa ta lalata wasu kwale-kwale da wuraren ajiyar kayayyakin aiki na barayin danyen mai. Gudanar da matatun mai ba bisa ka'ida ba ya zama ruwan dare a Nijeriya - daya daga cikin manyan kasashe masu arzikin mai a nahiyar Afirka. "Za a ci gaba da kai wannan samame har sai an samu galaba wajen dakatar ko rage ayyukan bata-gari," a cewar sanarwar da mai managa da yawun rundunar sojojin saman Nijeriya Edward Gabkwet ya fitar ranar Laraba. Ana yawan gudanar da ayyukan daruruwan haramtattun matatun mai a yankin Neja-Delta mai arzikin man fetur a Nijeriya. Kasar dai tana ci gaba da yaki don dakile masu haka haramtattun matatun mai a daidai lokacin da ake zargin cewa akwai hannun manyan 'yan siyasa da jami'an tsaro a wadannan munanan ayyuka. An lalata kwale-kwale da tafkunan ruwa da tankunan ajiyar mai a yayin samamen sojin. Nijeriya na da kusan ganga biliyan 37 na arzikin danyen mai, a cewar kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta Opec.