الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

Sojojin Nijeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda a Adamawa da Borno

Operation Hadin Kai ta dakile hare-haren ‘yan ta’adda a Arewa maso Gabas. Sojojin Rundunar Haɗin Gwiwa ta Operation Hadin Kai sun kashe ‘yan ta’adda da dama bayan dakile wasu hare-hare da aka shirya a Jihohin Adamawa da Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya. Mukaddashin Jami’in Watsa Labarai n...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:20 ص
Sojojin Nijeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda a Adamawa da Borno
لمحة سريعة

Operation Hadin Kai ta dakile hare-haren ‘yan ta’adda a Arewa maso Gabas. Sojojin Rundunar Haɗin Gwiwa ta Operation Hadin Kai sun kashe ‘yan ta’adda da dama bayan dakile wasu hare-hare da aka shirya a Jihohin Adamawa da Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya. Mukaddashin Jami’in Watsa Labarai n...

Operation Hadin Kai ta dakile hare-haren ‘yan ta’adda a Arewa maso Gabas. Sojojin Rundunar Haɗin Gwiwa ta Operation Hadin Kai sun kashe ‘yan ta’adda da dama bayan dakile wasu hare-hare da aka shirya a Jihohin Adamawa da Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya. Mukaddashin Jami’in Watsa Labarai na rundunar, Laftanar Solomon Atokolo, ya ce nasarar ta biyo bayan farmakin da sojojin suka kai wa ‘yan ta’addan a sassa daban-daban na yankin, lamarin da ya jawo musu asara mai yawa yayin da suke tserewa. A safiyar ranar 16 ga Janairun 2026, ‘yan ta’adda sun yi yunkurin kwace sansanin sintiri a Sabon Gari da ke Karamar Hukumar Madagali a Jihar Adamawa. Sai dai sojojin da ke wurin sun gaggauta tunkarar su tare da samun tallafi daga dakarun Gulak da kuma Rundunar Gaggawa ta Bataliya, lamarin da ya tilasta wa maharan janyewa ba tare da sojoji sun yi asarar rai ko kayan aiki ba. Bayan harin, sojojin sun ci gaba da binciken yankin domin gano nakiyoyi da sauran abubuwan fashewa da ‘yan ta’addan ka iya bari domin tabbatar da tsaron fararen hula da dakarun soji. Haka kuma a rana guda, ‘yan ta’adda sun kai wani hari kan sansanin soji na FOB da ke Azir a Jihar Borno. Sojojin sun tarbe su da wuta tare da samun goyon bayan Sojojin Sama na Nijeriya, wanda ya tilasta wa maharan janyewa. A yayin artabun, wasu harba-harban roka da ‘yan ta’addan suka yi sun haifar da gobara a wani ɓangare na sansanin, amma sojojin sun ci gaba da rike iko da wurin. Sojojin sun kuma kwato makamai da alburusai da dama daga hannun ‘yan ta’addan, ciki har da bama-baman mortar, abubuwan fashewa da aka ƙera a gida, da daruruwan harsasan bindiga. Tushen labari: Newstimehub