Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

Sojojin Nijeriya sun kashe 'yan ta'adda fiye da 100

A baya-bayan nan jami'an tsaron Nijeriya sun ƙara ƙaimi a yaƙin da suke yi da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya da masu garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa. Sojojin Nijeriya sun kashe 'yan ta'adda na ƙungiyar Boko Haram da ISWAP da masu garkuwa da mutane 101 a cikin mako guda. Kakakin ru...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:20
Sojojin Nijeriya sun kashe 'yan ta'adda fiye da 100
A taƙaice

A baya-bayan nan jami'an tsaron Nijeriya sun ƙara ƙaimi a yaƙin da suke yi da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya da masu garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa. Sojojin Nijeriya sun kashe 'yan ta'adda na ƙungiyar Boko Haram da ISWAP da masu garkuwa da mutane 101 a cikin mako guda. Kakakin ru...

A baya-bayan nan jami'an tsaron Nijeriya sun ƙara ƙaimi a yaƙin da suke yi da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya da masu garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa. Sojojin Nijeriya sun kashe 'yan ta'adda na ƙungiyar Boko Haram da ISWAP da masu garkuwa da mutane 101 a cikin mako guda. Kakakin rundunar tsaron Nijeriya, Manjo Janar Edward Buba, wanda ya bayyana hakan ranar Juma'a, ya ƙara da cewa sojoji sun kai samame a yankuna daban-daban na ƙasar a cikin mako guda. Buba ya ce wani kwamandan Boko Haram yana cikin waɗanda aka kashe a samamen. Bugu da ƙari, kakakin rundunar tsaron ya ce an ceto mutum 157 da 'yan ta'adda suka yi garkuwa da su sannan an kama 'yan ta'adda 182. Ya ce dakarun tsaron sun ƙwato makamai 71 da ababen hawa biyu da kuma tarin alburusai. Nijeriya ta daɗe tana fama da hare-hare daha mayaƙan Boko Haram da ISWAP, musamman a arewa maso gabashin ƙasar da kuma masu garkuwa da mutane a arewa maso yamma.