An Hallaka Abu Khalid Tare da ’Yan Ta’adda 10 a Farmakin Dare Sojojin Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Gabas ƙarƙashin Operation Hadin Kai sun kashe wani babban jagoran Boko Haram/ISWAP mai suna Abu Khalid a wani farmaki da aka kai da dare a Jihar Borno. TRT Hausa Abu Khalid, wanda shi ne mataimakin shugaban Boko Haram na biyu a Dajin Sambisa, an kashe shi ne tare da wasu ’yan ta’adda 10 yayin farmakin da sojojin Sector 1 suka kai da haɗin gwiwar ’yan Civilian Joint Task Force a yankin Komala na Karamar Hukumar Konduga. TRT Hausa Jami’in watsa labarai na rundunar, Laftanar Kanal Sani Uba, ya bayyana cewa farmakin ya biyo bayan kashe wani shahararren kwamandan Boko Haram/ISWAP mai suna Julaibib a yankin Gujba na Timbuktu Triangle, ƙasa da awanni 24 kafin wannan hari. TRT Hausa Uba ya ce Abu Khalid na daga cikin muhimman jagororin ’yan ta’adda, inda yake da alhakin tsara hare-hare da kula da kayan aiki a Dajin Sambisa, lamarin da ke nuna muhimmancin nasarar da aka samu. TRT Hausa A yayin farmakin, sojojin sun kwato bindigogin AK-47 guda biyar, da ƙundun harsasai, kekuna, kayayyakin abinci da kuma wasu muhimman kayan kiwon lafiya daga hannun ’yan ta’addan. TRT Hausa Rundunar ta tabbatar da cewa ba a samu asarar rai a ɓangaren sojoji ba, tare da jaddada cewa ana ci gaba da ayyukan tsabtace yankuna a Sambisa, Dutsen Mandara, Timbuktu Triangle da sauran maboyar Boko Haram da ISWAP a Arewa maso Gabas. TRT Hausa
Haber arşivi
Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.
Sojoji Sun Kashe Babban Jagoran Boko Haram a Sambisa
An Hallaka Abu Khalid Tare da ’Yan Ta’adda 10 a Farmakin Dare Sojojin Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Gabas ƙarƙashin Operation Hadin Kai sun kashe wani babban jagoran Boko Haram/ISWAP mai suna Abu Khalid a wani farmaki da aka kai da dare a Jihar Borno. TRT Hausa Abu Khalid, wanda shi ne matai...

Bu haberde ne var?
An Hallaka Abu Khalid Tare da ’Yan Ta’adda 10 a Farmakin Dare Sojojin Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Gabas ƙarƙashin Operation Hadin Kai sun kashe wani babban jagoran Boko Haram/ISWAP mai suna Abu Khalid a wani farmaki da aka kai da dare a Jihar Borno. TRT Hausa Abu Khalid, wanda shi ne matai...
