Home / News archive
News archive

This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.

Sojojin Nijeriya sun kashe ‘yan ta’adda 30, sun dawo da ‘yan gudun hijira 700

Operation Hadin Kai ta ƙara ƙaimi a yaƙin da Boko Haram da ISWAP Hedikwatar Tsaron Nijeriya ta ce dakarun rundunar Operation Hadin Kai sun kawar da fiye da ‘yan ta’adda 30 tare da taimaka wa fiye da ‘yan gudun hijira ‘yan Nijeriya 700 komawa gida cikin makon da ya gabata, sakamakon ƙara ƙaimi a a...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Updated 13/08/2026, 05:26:20
Sojojin Nijeriya sun kashe ‘yan ta’adda 30, sun dawo da ‘yan gudun hijira 700
At a glance

Operation Hadin Kai ta ƙara ƙaimi a yaƙin da Boko Haram da ISWAP Hedikwatar Tsaron Nijeriya ta ce dakarun rundunar Operation Hadin Kai sun kawar da fiye da ‘yan ta’adda 30 tare da taimaka wa fiye da ‘yan gudun hijira ‘yan Nijeriya 700 komawa gida cikin makon da ya gabata, sakamakon ƙara ƙaimi a a...

Operation Hadin Kai ta ƙara ƙaimi a yaƙin da Boko Haram da ISWAP Hedikwatar Tsaron Nijeriya ta ce dakarun rundunar Operation Hadin Kai sun kawar da fiye da ‘yan ta’adda 30 tare da taimaka wa fiye da ‘yan gudun hijira ‘yan Nijeriya 700 komawa gida cikin makon da ya gabata, sakamakon ƙara ƙaimi a ayyukan yaƙi da ta’addanci a arewa-maso-gabashin ƙasar. TRT Hausa Daraktan Harkokin Watsa Labarai na Tsaro, Maj-Gen Michael Onoja, ya ce nasarorin sun samo asali ne daga farmaki bisa bayanan sirri kan Boko Haram, ISWAP da JAS, tare da haɗin gwiwar sojin sama da ƙungiyoyin tsaro na yankin. TRT Hausa A yankin Timbuktu Triangle kusa da Kimba a ƙaramar hukumar Damboa ta Jihar Borno, sojoji sun kashe fiye da ‘yan ta’adda 20 ciki har da wani kwamanda da ake kira Julaibib, tare da rusa manyan wuraren tsare ‘yan ta’adda guda uku da ceto mutane 70. TRT Hausa Haka kuma an samu ƙarin nasarori a Gwoza (Borno), Hong da Mubi North (Adamawa), inda aka kama masu satar mutane, aka ceto waɗanda aka sace, tare da ƙwato makamai da kayan soji. TRT Hausa Rundunar ta kuma taimaka wajen dawo da rukuni na biyu na kusan ‘yan gudun hijira ‘yan Nijeriya 700 daga Kamaru ta iyakar Banki a ƙaramar hukumar Bama ta Jihar Borno, tare da samar da cikakken tsaro a duk tsawon aikin. TRT Hausa