Rundunar Sojin Nijar a ranar Lahadi ta sanar da kashe Abdoulaye Souleymane Idouwal wanda ta bayyana a matsayin “babban mai faɗa a ji a ƙungiyar IS”. Rundunar Sojin Nijar a ranar Lahadi ta tabbatar da kashe wani babban mamba a ƙungiyar IS da iƙirarin jihadi a wani samame da ƙasar sojojin ƙasar suka kai. Rundunar ta sanar da cewa dakarunta sun kai samame kan ‘yan ta’addan a ranar Juma’a a yankin Tillaberi a tsakanin iyakokin Niger da Mali da Burkina Faso wadanda ke fama da rikicin ta’addanci. Sojojin sun bayyana cewa sun kashe Abdoulaye Souleymane Idouwal wanda suka bayyana a matsayin “mai faɗa a ji a ƙungiyar IS”. Rundunar ta kuma bayyana cewa ta kashe ‘yan ta'adda tara da kuma kama 31 a wani samame da ta kai a yankin a ranar Alhamis. Sojojin sun yi iƙirarin kassara hanyar sufurin ‘yan ta’addan tare da daƙile hanyoyin sadarwar ‘yan ta’addan. ‘Yan ta’addan na yawan kai wa farar hula hari a yankin na Tillaberi, wanda hakan ke raba mutane da muhallansu. Nijar na ƙarƙashin mulkin soji waɗanda suka ƙwace mulki a Yulin bara, inda suka ce taɓarɓarewar tsaro na daga cikin dalilan ƙwace mulkin. Sojojin na Nijar na yaƙi da ‘yan ta’addan Boko Haram da kuma takwarorinsu na ISWAP a wasu yankunan ƙasar.
Arquivo de notícias
Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.
Sojojin Nijar sun kashe wani 'babban ɗan ƙungiyar IS' a Tillaberi
Rundunar Sojin Nijar a ranar Lahadi ta sanar da kashe Abdoulaye Souleymane Idouwal wanda ta bayyana a matsayin “babban mai faɗa a ji a ƙungiyar IS”. Rundunar Sojin Nijar a ranar Lahadi ta tabbatar da kashe wani babban mamba a ƙungiyar IS da iƙirarin jihadi a wani samame da ƙasar sojojin ƙasar suk...

Em resumo
Rundunar Sojin Nijar a ranar Lahadi ta sanar da kashe Abdoulaye Souleymane Idouwal wanda ta bayyana a matsayin “babban mai faɗa a ji a ƙungiyar IS”. Rundunar Sojin Nijar a ranar Lahadi ta tabbatar da kashe wani babban mamba a ƙungiyar IS da iƙirarin jihadi a wani samame da ƙasar sojojin ƙasar suk...
