Mehana na daga cikin yankuna shida da aka kai hari a yankin Tillaberi na Jamhuriyar Nijar mai iyaka da Mali da Burkina Faso kuma ya zama maɓoyar mayaka masu ikirarin jihadi da ke da alaƙa da kungiyar IS da Al-Qaeda. An kashe fararen hula 15 tare da jikkata wasu da dama a wasu hare-haren ta'addanci da aka kai a ƙauyukan yammacin Nijar da ke kusa da iyakar Burkina Faso a farkon makon nan, in ji sanarwar da rundunar sojin ƙasar ta fitar a yammacin jiya Laraba. "A yankin Mehana, 'yan ta'adda sun kai munanan hare-hare da dama kan fararen hular da ba su da kariya, inda aka samu mummunar asara," in ji sanarwar, inda aka ce an kashe mutum 14 a wata rana da ba a tantance ba, lamarin da ya biyo bayan mutuwar akalla wani farar hula guda a ranar Talata duk a yanki ɗaya. Mehana na daga cikin yankuna shida da aka kai hari a yankin Tillaberi na Jamhuriyar Nijar mai iyaka da Mali da Burkina Faso kuma ya zama maɓoyar mayaka masu ikirarin jihadi da ke da alaƙa da kungiyar IS da Al-Qaeda. Ƙungiyoyin 'yan ta'adda na yawan kai wa fararen hula hari a Mehana, lamarin da ke raba mutane da dama da muhallansu. Har ila yau, a yankin Tillaberi a ranar Talata, wani farar hula daya ya mutu, wasu uku kuma suka jikkata, a wani ƙazamin rikici da ya ɓarke tsakanin sashen binciken sojoji da ‘yan ta’adda a kusa da garin Chatoumane, in ji rundunar. “Jami’an tsaro sun dauki matakin da ya dace, inda suka kashe ‘yan ta’adda da dama,” in ji sojojin. Kasar Nijar dai na karkashin jagorancin shugabanin sojoji ne da suka ƙwace mulki a watan Yuli, inda suka ce sun yi hakan ne saboda yadda matsalar tsaro ke ƙara tabarbarewa. Nijar na kuma na fuskantar tashin hankali daga mayakan Boko Haram da kuma abokan hamayyarsu na IS da ke yankin yammacin Afirka daga yankin Diffa da ke kudu maso gabashin Nijeriya. A cewar Acled, wata cibiya mai bin diddigin rikice-rikice, masu ikirarin jihadi sun kashe fararen hula da sojoji kusan 1,500 a cikin shekarar da ta gabata a Nijar, idan aka kwatanta da 650 a cikin shekara zuwa Yuli 2023.
Arquivo de notícias
Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.
Sojojin Nijar sun ce an kashe fararen hula 15 a hare-haren 'yan ta'adda a yammacin ƙasar
Mehana na daga cikin yankuna shida da aka kai hari a yankin Tillaberi na Jamhuriyar Nijar mai iyaka da Mali da Burkina Faso kuma ya zama maɓoyar mayaka masu ikirarin jihadi da ke da alaƙa da kungiyar IS da Al-Qaeda. An kashe fararen hula 15 tare da jikkata wasu da dama a wasu hare-haren ta'addanc...

Em resumo
Mehana na daga cikin yankuna shida da aka kai hari a yankin Tillaberi na Jamhuriyar Nijar mai iyaka da Mali da Burkina Faso kuma ya zama maɓoyar mayaka masu ikirarin jihadi da ke da alaƙa da kungiyar IS da Al-Qaeda. An kashe fararen hula 15 tare da jikkata wasu da dama a wasu hare-haren ta'addanc...
