Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

Sojojin Mali sun sanar da kama wani jagoran ƙungiyar ta'addanci

Sojojin na zarginsa da kitsa muggan hare-hare na zalunci a yankunan Menaka da Gao da ke arewa maso gabashin ƙasar, da kuma hare-hare kan sojojin ƙasar. Rundunar Sojin Mali a ranar Asabar ta sanar da cewa dakarunta sun kama wasu mutum biyu, inda ɗaya daga cikinsu jagora ne a wata ƙungiyar ta'addan...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:20
Sojojin Mali sun sanar da kama wani jagoran ƙungiyar ta'addanci
Kwa muhtasari

Sojojin na zarginsa da kitsa muggan hare-hare na zalunci a yankunan Menaka da Gao da ke arewa maso gabashin ƙasar, da kuma hare-hare kan sojojin ƙasar. Rundunar Sojin Mali a ranar Asabar ta sanar da cewa dakarunta sun kama wasu mutum biyu, inda ɗaya daga cikinsu jagora ne a wata ƙungiyar ta'addan...

Sojojin na zarginsa da kitsa muggan hare-hare na zalunci a yankunan Menaka da Gao da ke arewa maso gabashin ƙasar, da kuma hare-hare kan sojojin ƙasar. Rundunar Sojin Mali a ranar Asabar ta sanar da cewa dakarunta sun kama wasu mutum biyu, inda ɗaya daga cikinsu jagora ne a wata ƙungiyar ta'addanci a yankin Sahel. Rundunar sojin ta kuma sanar da cewa ta kashe mayaƙan ƙungiyar ta'addancin da dama a lokacin da ta kai wani samame a arewacin ƙasar. A wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar, ta bayyana cewa ta kama "Mahamad Ould Erkehile wanda aka fi sani da Abu Rakia", da kuma "Abu Hash" wanda suka ce shi ne ke jagorantar ƙungiyar. Sojojin na zarginsa da kitsa muggan hare-hare na zalunci a yankunan Menaka da Gao da ke arewa maso gabashin ƙasar, da kuma hare-hare kan sojojin ƙasar. Yanke hulɗa da Faransa Rashin tsaro ya yi ƙamari a Mali a shekarar 2012 inda ya bazu zuwa Nijar da Burkina Faso. Shugabannin sojin ƙasar sun yanke hulɗa da Faransa wadda ita ce ta yi musu mulkin mallaka inda suka karkata zuwa ga Rasha.