Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 81 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa fiye da 20,674, galibinsu mata da kananan yara, sannan sun jikkata fiye da mutum 54,536. 1616 GMT — Sojojin Isra'ila 40 ne suka jikkata a yakin Gaza cikin sa'o'i 24 da suka gabata, in ji sojoji Rundunar sojin Isra'ila ta ce akalla sojoji 40 ne suka jikkata a fadan da aka gwabza a Gaza cikin sa'o'i 24 da suka gabata. Sanarwar da rundunar sojin ta fitar ta ce sojoji biyar na cikin mawuyacin hali. Alkaluman sojoji sun ce akalla sojoji 874 ne suka jikkata tun bayan da Isra'ila ta fadada ayyukanta na kasa a Gaza a ranar 27 ga watan Oktoba. Sojojin Isra'ila sun kuma ce an kashe sojoji 492 tun bayan barkewar rikicin Gaza a ranar 7 ga watan Oktoba. 1600 GMT — Za a sake shafe watanni Isra'ila na yaki a Gaza — Shugaban sojoji Yakin da Isra'ila take yi da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas a Gaza zai dauki tsawon watanni da dama ba a gama ba," in ji babban hafsan sojin Isra'ila Herzi Halevi. Yakin "zai ci gaba da wanzuwa na tsawon wasu watanni, kuma za mu yi aiki da hanyoyi daban-daban domin a kiyaye nasarorin da muka samu na dogon lokaci", in ji Halevi a wani taron manema labarai da aka watsa ta talabijin. 1200 GMT — Kasa mayar wa Isra'ila martani da Iran ta yi alama ce ta tsor o : Jami'in Houthi Wani babban jami'in Houthi na kasar Yaman ya bayyana cewa, shirun da Iran ta yi da rashin mayar da martani ga Isra'ila, ana iya kallonta a matsayin "alama ta rauni da tsoro da kuma fargabar yin arangama". Abdulsalam Jahaf, mamba a kwamitin tsaro na majalisar shura ta kasar Yemen ya bayyana a hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin bayan kisan Sayyed Razi Mousavi, babban kwamandan dakarun juyin juya halin Musulunci na Iran. Jahaf ya wallafa a shafinsa na X cewa "Tun da Yahudawan masu tsaurin akidar kafa kasar Isra'ila sun fara wuce gona da iri wajen kai wa Iran hari, to dole ne Iran ta mayar da martani. Ba makawa tsoron yakin kai tsaye zai haifar da hakan. Iran ba ta da wani zabi illa daukar fansa." Sanarwar da Iran ta yi na cewa duk da tana da 'yancin ramuwar gayya amma ba za ta yi ba, "ko shakka babu mataki ne na hikima" kuma "ba yana nufin ba za ta iya mayar da martani ba ne ko kadan," in ji babban jami'in. Ya kara da cewa "Muna sane da cewa yaki zai haifar da mummunan sakamako, amma yin shiru zai fi haifar da sakamako mafi girma," ya ƙara da cewa. 0913 GMT — Isra'ila ta kama wata babbar 'yar siyasar Falasdinu Khalida Jarrar Isra’ila a ranar Talata ta kama wata babbar ‘yar siyasar Falasdinu Khalida Jarrar daga gidanta da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan. Wadanda suka shaida lamarin sun bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa dakarun na Isra’ila sun kai samame birnin Al-Bireh tare da kama Jarrar bayan gudanar da bincike a gidanta. Isra’ila ta sha kama ta, inda lokaci na karshe da aka sake ta shi ne Satumbar 2021 bayan ta shafe shekara biyu a tsare. 2316 GMT — Isra'ila ta kashe tare da jikkata Falasdinawa 750 a Gaza cikin sa'o'i 24 Akalla Falasdinawa 250 aka kashe tare da jikkata wasu 500 sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai a zirin Gaza cikin sa'o'i 24 da suka gabata, in ji ma'aikatar lafiya ta Gaza. A cikin wata sanarwa da kakakin ma'aikatar Ashraf al-Qudra ya fitar, ya ce kungiyoyin likitocin ba su iya kula da dukkan wadanda suka jikkata da suka isa asibitoci ba, yayin da ya ce suna fama da kula da nau'ikan raunukan da ba su gani ba a yaƙin da suka gabata. Akalla Falasdinawa 250 aka kashe tare da jikkata wasu 500 sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai a zirin Gaza cikin sa'o'i 24 da suka gabata / Hoto: Reuters Ya ƙara da cewa adadin gadajen kwantar da marasa lafiya a asibitocin da ke aiki a kudancin Zirin Gaza ya kai kashi 350 cikin 100. Al-Qudra ya kuma yi nuni da cewa, agajin jinƙai da na jinya da ke isa Gaza ba ya biyan buƙatun asibitocin ba. Da sanyin safiyar Talata, mazauna Falasdinu sun ba da rahoton wasu hare-hare ta sama a kusa da asibitin Nasser da ke Khan Younis, cibiyar kiwon lafiya mafi girma a kudancin Gaza. Jami'an kiwon lafiya na Falasdinu sun ce mutane bakwai ne suka mutu a wani harin sama da jiragen yaƙin Isra'ila suka kai a wani gida da ke unguwar Al-Amal a Khan Younis. 0239 GMT — Amurka ta kai hari kan wuraren da ta ce sojojin da Iran ke mara wa baya a Iraki ne ke amfani da su Sojojin Amurka sun kai hare-hare a wasu wurare uku da sojojin da Iran ke mara wa baya ke amfani da su a Iraƙi, bayan wani harin da aka raunata ma'aikatan Amurka a safiyar yau, in ji Sakataren Tsaro, Lloyd Austin. Austin a cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce: Sojojin Amurka sun kai farmakin da suka dace kuma daidai gwargwado kan wasu wurare uku da Kataeb Hezbollah ke amfani da su da kuma kungiyoyin da ke da alaƙa da su a Iraƙi. “Wadannan madaidaitan hare-haren martani ne ga jerin hare-haren da dakarun sa kai da Iran ke ɗaukar nauyin kai wa jami’an Amurka a Iraƙi da Syria, ciki har da harin Kataeb Hezbollah mai alaƙa da Iran da ƙungiyoyin da ke da alaƙa da Iran a sansanin jiragen sama na Arbil da safiyar yau," ya faɗa. 2342 GMT — Shugaban Isra'ila ya ziyarci sojojin da ke kusa da Gaza Shugaban Isra'ila Isaac Herzog ya ziyarci sojojin da suka mamaye yankin da ke kusa da Gaza a ranar Litinin. Shugaban Isra'ila Isaac Herzog ya ziyarci sojojin da suka mamaye yankin da ke kusa da Gaza a ranar Litinin. Herzog ya wallafa wani hoto a shafinsa na X wanda ke nuna shi yana rubuta "Mun amince da ku," a cikin harshen Ibrananci a kan harsasan bindigogi don nuna goyon baya ga kokarinsu. "Ina so in gode muku, ba abu ne mai sauki ba ko kadan, kuma ba abin wasa ba ne cewa sama da watanni biyu mutane suna nan," ya shaida wa sojojin. Ya kara da cewa dole ne sojoji su samu cikakken goyon baya yayin da suke kan gaba da kuma da zarar sun dawo daga bakin aiki.
Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.
Sojojin Isra'ila 40 ne suka jikkata a yakin Gaza cikin sa'o'i 24 da suka gabata - Rundunar soji
Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 81 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa fiye da 20,674, galibinsu mata da kananan yara, sannan sun jikkata fiye da mutum 54,536. 1616 GMT — Sojojin Isra'ila 40 ne suka jikkata a yakin Gaza cikin sa'o'i 24 da suka gabata, in ji sojoji Rundunar...

Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 81 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa fiye da 20,674, galibinsu mata da kananan yara, sannan sun jikkata fiye da mutum 54,536. 1616 GMT — Sojojin Isra'ila 40 ne suka jikkata a yakin Gaza cikin sa'o'i 24 da suka gabata, in ji sojoji Rundunar...
