Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

Sojojin Amurka Sun Isa Maiduguri Don Tallafin Tsaro

Tura sojojin na nuni da sabuwar alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka Jiragen rundunar sojin Amurka guda uku masu ɗauke da sojoji da makamai sun isa Maiduguri, babban birnin Jihar Borno a Nijeriya , abin da ke nuna sabuwar alaƙar soji da tsaro da za ta mayar da hankali kan tallafi na tsaro, in...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:20
Sojojin Amurka Sun Isa Maiduguri Don Tallafin Tsaro
Kwa muhtasari

Tura sojojin na nuni da sabuwar alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka Jiragen rundunar sojin Amurka guda uku masu ɗauke da sojoji da makamai sun isa Maiduguri, babban birnin Jihar Borno a Nijeriya , abin da ke nuna sabuwar alaƙar soji da tsaro da za ta mayar da hankali kan tallafi na tsaro, in...

Tura sojojin na nuni da sabuwar alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka Jiragen rundunar sojin Amurka guda uku masu ɗauke da sojoji da makamai sun isa Maiduguri, babban birnin Jihar Borno a Nijeriya , abin da ke nuna sabuwar alaƙar soji da tsaro da za ta mayar da hankali kan tallafi na tsaro, in ji jami’ai. TRT Hausa Jami’ai a Hedikwatar Tsaron Nijeriya sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa kimanin sojojin Amurka 100 sun isa Nijeriya tsakanin Alhamis da Lahadi a matsayin rukunin farko, tare da ƙarin jirage da ake sa ran za su iso a makonni masu zuwa. TRT Hausa Wani jami’in tsaro ya ce sojojin Amurka za su mayar da hankali ne kan ayyukan da ba na yaƙi ba, inda za su yi aiki daga cibiyoyin bayar da umarni domin tallafa wa ƙoƙarin tsaro na Nijeriya, ba tare da shiga faɗa kai tsaye ba. TRT Hausa Tun da farko, kakakin Hedikwatar Tsaron Nijeriya, Manjo Janar Samaila Uba, ya bayyana cewa sojojin Amurka ba za su yi aikin yaƙi kai tsaye ba, illa dai bayar da goyon bayan fasaha da horo. TRT Hausa Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun matsin lamba daga shugaban Donald Trump , wanda ya soki yadda Nijeriya ke tafiyar da martani ga hare-haren da ake kai wa wasu al’ummomi. TRT Hausa Gwamnatin Nijeriya ta yi watsi da wannan zargi, tana mai cewa rikicin tsaro na shafar Musulmai da Kiristoci baki ɗaya, yayin da take ƙara ɗaukar matakan tsaro ciki har da tura dakaru na musamman zuwa jihohin Filato da Taraba. TRT Hausa Hukumomin Amurka sun nuna cewa tura sojojin na wucin-gadi ne, duk da cewa ba a fayyace tsawon lokacin zamansu a Nijeriya ba. TRT Hausa