Home / News archive
News archive

This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.

Shugaban Zimbabwe ya dakatar da bulaguro saboda barazanar hari a filin jirgin sama

Shugaban kasar Emmerson Mnangagwa ya dakatar da tafiyar tasa ne saboda ba da damar gudanar da bincike, a cewar hukumomi. Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya dakatar da tafiyarsa zuwa Victoria Falls a ranar Juma'a saboda barazanar kai wani hari da ba a tantance ba tukunna a filayen jirag...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Updated 13/08/2026, 05:26:20
Shugaban Zimbabwe ya dakatar da bulaguro saboda barazanar hari a filin jirgin sama
At a glance

Shugaban kasar Emmerson Mnangagwa ya dakatar da tafiyar tasa ne saboda ba da damar gudanar da bincike, a cewar hukumomi. Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya dakatar da tafiyarsa zuwa Victoria Falls a ranar Juma'a saboda barazanar kai wani hari da ba a tantance ba tukunna a filayen jirag...

Shugaban kasar Emmerson Mnangagwa ya dakatar da tafiyar tasa ne saboda ba da damar gudanar da bincike, a cewar hukumomi. Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya dakatar da tafiyarsa zuwa Victoria Falls a ranar Juma'a saboda barazanar kai wani hari da ba a tantance ba tukunna a filayen jiragen saman kasar, a cewar mai magana da yawunsa. A safiyar ranarJuma'a ne aka sanar da hukumomin filin jirgin saman Zimbabwe wani sakon imel da aka tura wa kamfanin jiragen sama na Fastjet kan "barazanar kai harin makamai da bam" a filayen jiragen saman Zimbabwe, in ji mai magana da yawun shugaban kasar George Charamba a cikin wata sanarwa da ya fitar. “A matsayin wani mataki na taka tsantsan, tsarin tsaron kasar a halin yanzu na cikin shirin ko-ta-kwana biyo bayan wannan sako wanda kuma ake kan binciken tushen sa da sahihancin sa,” inji shi. A cewar Charamba, Shugaba Mnangagwa na shirin gabatar da jawabi ne a wani taro a garin Victoria Falls amma ya dakatar da tafiyarsa domin a samu damar gudanar da bincike, ya kuma buƙaci jama’a da su kwantar da hankulansu. An ɗauki tsauraran matakan ko ko-ta-kwana "Yayin da ƙasarmu ke cikin zaman lafiya, kuma an samar da tsaro a dukka tashoshin jiragen ruwanmu, akwai bukatar a dauki irin wannan sanarwar yiwuwar kai hare-haren ta'addanci da muhimmanci," a cewar sanarwar. Tun da farko kafofin yada labarai na kasar suka rawaito cewa a ranar Juma’a jirgin Shugaba Mnangagwa ya juya mintuna kadan kafin ya sauka a filin jirgin saman Victoria Falls, sannan ya koma Harare babban birnin kasar. An tsare wani jirgin Air Zimbabwe dauke da fasinjoji a Victoria Falls, yayin da wani jirgin Kenya Airways ya juya saukarsa zuwa Livingstone da ke kasar Zambiya, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka rawaito.