Ana Sayfa / Haber arşivi
Haber arşivi

Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.

Erdoğan Ya Gana da Yarima mai Jiran Gado na Saudiyya a Riyad

Ziyarar na daga cikin rangadin shugaban Turkiyya a ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya gana da Yarima mai jiran gadon Saudiyya Mohammed bin Salman (MBS) a birnin Riyad a ranar Talata, kamar yadda Shugaban Sadarwa na Turkiyya, Burhanettin Duran, ya bayyana. T...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Güncellendi 13.08.2026 05:26:20
Erdoğan Ya Gana da Yarima mai Jiran Gado na Saudiyya a Riyad
Bu haberde ne var?

Ziyarar na daga cikin rangadin shugaban Turkiyya a ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya gana da Yarima mai jiran gadon Saudiyya Mohammed bin Salman (MBS) a birnin Riyad a ranar Talata, kamar yadda Shugaban Sadarwa na Turkiyya, Burhanettin Duran, ya bayyana. T...

Ziyarar na daga cikin rangadin shugaban Turkiyya a ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya gana da Yarima mai jiran gadon Saudiyya Mohammed bin Salman (MBS) a birnin Riyad a ranar Talata, kamar yadda Shugaban Sadarwa na Turkiyya, Burhanettin Duran, ya bayyana. TRT Hausa Erdogan ya kai ziyarar aiki Saudiyya tare da matarsa Emine Erdoğan da manyan ministoci ciki har da Ministan Harkokin Waje Hakan Fidan, Ministan Kuɗi Mehmet Şimşek, Ministan Tsaro Yaşar Güler da wasu jami’ai. TRT Hausa Ba a fitar da cikakken bayani kan abin da aka tattauna a ganawar ta sirri tsakanin Erdogan da MBS ba, kamar yadda hukumomin Turkiyya suka bayyana. TRT Hausa Bayan ganawar, Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ya shirya wa shugaban Turkiyya liyafar cin abinci ta musamman a Fadar Al-Yamamah a matsayin girmamawa. TRT Hausa Tun da farko a ranar, Sarkin Saudiyya Salman bin Abdulaziz ya tarbi Erdogan a wani bikin maraba da aka shirya masa a hukumance. TRT Hausa Ziyarar Saudiyya ita ce mataki na farko a rangadin shugaban Turkiyya a yankin, inda ake sa ran hakan zai ƙara ƙarfafa alaƙar diflomasiyya da tattalin arziki tsakanin ƙasashen. TRT Hausa Daga Riyad, Erdogan zai tafi Alkahira a ranar Laraba bisa gayyatar Shugaban Masar Abdel Fattah el-Sisi, domin jagorantar taron Majalisar Haɗin Kai ta Manyan Matakai tsakanin Turkiyya da Masar. TRT Hausa A Masar, Erdogan da Sisi za su tattauna alaƙar ƙasashensu da kuma batutuwan yankin da na duniya, musamman halin da ake ciki a Falasdinu, tare da halartar Taron Kasuwanci na Turkiyya da Masar. TRT Hausa