Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

Shugaban Turkiyya Erdogan ya ƙarbi baƙuncin shugaban Hamas a Istanbul

Erdogan ya jaddada cewa Ankara na ci gaba da aiki babu dare babu rana a fannin diflomasiyya domin jawo hankalin duniya game da gallazawar da ake yi wa Falasɗinawa, da kuma buƙatar tsagaita wuta nan-take. Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya karɓi baƙuncin shugaban ƙungiyar Hamas da ke...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:20
Shugaban Turkiyya Erdogan ya ƙarbi baƙuncin shugaban Hamas a Istanbul
Kwa muhtasari

Erdogan ya jaddada cewa Ankara na ci gaba da aiki babu dare babu rana a fannin diflomasiyya domin jawo hankalin duniya game da gallazawar da ake yi wa Falasɗinawa, da kuma buƙatar tsagaita wuta nan-take. Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya karɓi baƙuncin shugaban ƙungiyar Hamas da ke...

Erdogan ya jaddada cewa Ankara na ci gaba da aiki babu dare babu rana a fannin diflomasiyya domin jawo hankalin duniya game da gallazawar da ake yi wa Falasɗinawa, da kuma buƙatar tsagaita wuta nan-take. Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya karɓi baƙuncin shugaban ƙungiyar Hamas da ke fafutukar kare ƴancin Falasɗinawa Ismail Haniyeh a Istanbul inda suka tattauna kan hare-haren da Isra'ila take ci gaba da kaiwa Gaza. A ganawar da suka yi ranar Asabar, shugabannin sun tattauna kan matakan da suka kamata a ɗauka don tabbatar da kai kayan agaji Gaza ba tare da tarnaƙi ba, da kuma yadda za a samu dawwamammen zaman lafiya a yankin. Erdogan ya jaddada cewa Ankara na ci gaba da aiki babu dare babu rana a fannin diflomasiyya domin jawo hankalin duniya game da gallazawar da ake yi wa Falasɗinawa, da kuma buƙatar tsagaita wuta nan-take. Da yake tsokaci game da jijiyoyin wuyan da ake tayarwa tsakanin Isra'ila da Iran, ya ce bai kamata hakan ya kawar da hankulan duniya game da ɓarnar da Isra'ila take tafkawa a Gaza ba. Erdogan ya ce Turkiyya na yin dukkan abin da ya dace wajen kafa ƙasar Falasɗinu domin kuwa hakan ne kawai zai wanzar da zaman lafiya a yankin, yana mai shan alwashin tabbatar da ganin an hukunta Isra'ila kan kisan ƙare-dangi da take aikatawa. Turkiyya na kan gaba a ƙasashen da ke kai kayan agaji Gaza inda kawo yanzu ta aika da tan dubu 45. Kazalika ƙasar ta aiwatar da takunkumai daban-daban da aka ƙaƙaba wa Isra'ila, ciki har da dakatar da cinikayya.