Shugaban Turkiyya ya ce yana fatan Maulidin Manzon Allah SAW zai kawo kwanciyar hankali da albarka ga dukkan mutane. Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya aika da saƙon fatan alkhairi saboda zuwan Maulidin Annabi Muhammad SAW, yana bayyana fatan cewa maulidin zai kawo kwanciyar hankali da albarka, ba ga Musulmi kaɗai ba, har ma ga duka 'yan adam. "A wannan lokaci na musamman da ake murnar kewayowar watan haihuwar Annabi, ina ƙara nuna girmamawa ga masoyinmu Annabi Muhammad, jagoranmu kuma shugabanmu, da cikakkiyar mutuntawa da ganin girma," kamar yadda ya wallafa a shafukansa na sada zumunta ranar Asabar. "Ina addu'a da fatan daren Maulidin ya kawo alkhairai da albarka ga Musulmai da duniya baki ɗaya." Veladet-i Nebi’nin yıl dönümünde rehberimiz, önderimiz, uğruna can vereceğimiz maşukumuz Hazreti Peygamber Efendimizi büyük bir ihtiramla, hürmetle yâd ediyorum. Leyle-i Mevlid’in Müslümanların yanı sıra tüm insanlık için hayırlar getirmesini temenni ediyorum. pic.twitter.com/ywwgGriL4p — Recep Tayyip Erdoğan (@RTErdogan) September 14, 2024 Musulmai a faɗin duniya suna yin bikin Maulidin Annabi SAW a ranar 12 ga watan Rabi-ul-Awwal, inda ranar ta bambanta daga ƙasa zuwa ƙasa, saboda bambancin lokaci. A lokacin maulidin, Musulmai na yin abubuwa da dama na nuna farin ciki, da suka haɗa da karatun Alƙur'ani, da addu'o'i, da halartar wuraren jawabai dangane da rayuwar Manzon Allah SAW da koyarwarsa, da gudanar da tarurruka da raba abinci. Ana bayar da hutun ranar a ƙasashe da dama da Musulmai ke da rinjaye, da suka haɗa da Pakistan da Indonesia da Malaysia da Bangladesh da Masar da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da wasu bangarori na Indiya.
أرشيف الأخبار
يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.
Shugaban Turkiyya Erdogan ya aike da sakon murnar zuwan Maulidi
Shugaban Turkiyya ya ce yana fatan Maulidin Manzon Allah SAW zai kawo kwanciyar hankali da albarka ga dukkan mutane. Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya aika da saƙon fatan alkhairi saboda zuwan Maulidin Annabi Muhammad SAW, yana bayyana fatan cewa maulidin zai kawo kwanciyar hankali da alb...

لمحة سريعة
Shugaban Turkiyya ya ce yana fatan Maulidin Manzon Allah SAW zai kawo kwanciyar hankali da albarka ga dukkan mutane. Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya aika da saƙon fatan alkhairi saboda zuwan Maulidin Annabi Muhammad SAW, yana bayyana fatan cewa maulidin zai kawo kwanciyar hankali da alb...
