Mogadishu ta bayyana yarjejeniyar a matsayin ‘haramtacciya,’ sannan ta kira a gudanar da taron gaggawa na kasashen duniya kan lamarin. Shugaban Somalia Hassan Sheikh Mohamud ya sanya hannu kan wata doka da ta haramta wa yankin Somalilanda da ya balle daga kasar bai wa Ethiopia damar yin amfani da tashar jiragen ruwa. Ya sanya hannu a kan dokar ne a Mogadishu, babban birnin kasar, a gaban shugaban Majalisar Dattawan Somalia Abdi Hash da takwaransa na Majalisar Wakilai Sheikh Adan Mohamed Nur. “Bayan samun goyon bayan 'yan majalisar dokokinmu da kuma al'ummarmu, wannan doka wata shaida ce da ke nuna jajircewarmu wajen tabbatar da hadin-kan kasa da kasancewarmu kasa mai cin gashin kanta kamar yadda dokokin duniya suka tsara,” in ji Mohamud a sakon da ya wallafa a shafin X. Turkiyya ta damu game da yarjejeniyar da Ethiopia da Somaliland suka kulla Ministan Watsa Labarai Daud Aweis dokar tana nuna matsayin Mogadishu a hukumance da kuma “yin kakkausan suka kan masu neman yin kutse a kasar Somalia.” Suldan I. Mohamed, wani mai sharhi kan harkokin siyasa, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa sanya hannu kan dokar wani martani ne mai karfi daga 'yan majalisun dokokin da gwamnatin Somalia.
أرشيف الأخبار
يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.
Shugaban Somalia ya sa hannu a dokar da ta haramta wa Somaliland bai wa Ethiopia damar amfani da tashar jiragen ruwa
Mogadishu ta bayyana yarjejeniyar a matsayin ‘haramtacciya,’ sannan ta kira a gudanar da taron gaggawa na kasashen duniya kan lamarin. Shugaban Somalia Hassan Sheikh Mohamud ya sanya hannu kan wata doka da ta haramta wa yankin Somalilanda da ya balle daga kasar bai wa Ethiopia damar yin amfani da...

لمحة سريعة
Mogadishu ta bayyana yarjejeniyar a matsayin ‘haramtacciya,’ sannan ta kira a gudanar da taron gaggawa na kasashen duniya kan lamarin. Shugaban Somalia Hassan Sheikh Mohamud ya sanya hannu kan wata doka da ta haramta wa yankin Somalilanda da ya balle daga kasar bai wa Ethiopia damar yin amfani da...
