الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

Shugaban Senegal Macky Sall ya ɗaga zaɓen ƙasar da za a yi a Fabrairu

Shugaban ƙasar ya ce matsaloli da ke tattare da jerin sunayen ƴan takara na daga cikin dalilan da suka sa aka ɗaga wannan zaɓen. Shugaban Senegal ya sanar da ɗage zaɓen ƙasar wanda aka yi niyyar gudanarwa a ranar 25 ga watan Fabrairun 2024. Shugaban ƙasar Macky Sall ne ya sanar da hakan a wani ja...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:20 ص
Shugaban Senegal Macky Sall ya ɗaga zaɓen ƙasar da za a yi a Fabrairu
لمحة سريعة

Shugaban ƙasar ya ce matsaloli da ke tattare da jerin sunayen ƴan takara na daga cikin dalilan da suka sa aka ɗaga wannan zaɓen. Shugaban Senegal ya sanar da ɗage zaɓen ƙasar wanda aka yi niyyar gudanarwa a ranar 25 ga watan Fabrairun 2024. Shugaban ƙasar Macky Sall ne ya sanar da hakan a wani ja...

Shugaban ƙasar ya ce matsaloli da ke tattare da jerin sunayen ƴan takara na daga cikin dalilan da suka sa aka ɗaga wannan zaɓen. Shugaban Senegal ya sanar da ɗage zaɓen ƙasar wanda aka yi niyyar gudanarwa a ranar 25 ga watan Fabrairun 2024. Shugaban ƙasar Macky Sall ne ya sanar da hakan a wani jawabi da ya yi wa ƙasar a Dakar babban birnin ƙasar inda ya ce an ɗage zaɓen sakamakon wasu matsaloli da ke tattare da jerin sunayen ƴan takar A Nuwambar bara ne Mista Sall ya saka ranar 25 ga watan Fabrairu a matsayin ranar zaɓen ƙasar inda ƴan takara 20 za su fafata a zaɓen sai dai a cikin mutanen babu sunayen wasu manyan ƴan adawa. Sai dai a jawabin da Sall ya yi a ranar Lahadi, ya ce ya saka hannu kan wata doka wadda ta yi watsi da hanyar da aka bi wurin saka ranar a baya inda ya ce ƴan majalisa za su gudanar da bincike kan wasu alƙalai biyu dangane da martabarsu sakamakon suna da alamar tambaya a tattare da su ta fuskar zaɓe. Sall ya sha nanata cewa zai miƙa mulki a watan Afrilu zuwa ga wanda ya ci zaɓe. Bayan sanar da cewa ba zai yi takara ba a karo na uku, Sall ya bayyana Firaiminista Amadou Ba wanda ɗan jam’iyyarsa ne a matsayin magajinsa. Kotun ƙasar ta cire sunayen gomman ƴan takara da zaɓen daga ciki har da ɗan adawar nan Ousmane Sonko da Karim Wade, ɗan gidan tsohon shugaban ƙasar Abdoulaye Wade.