Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

Shugaban Nijeriya ya ba da kyautar dala $100,000 da lambar yabo ga 'yan wasan D’Tigress

Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ayyana kyautar dala $100,000 da lambobin yabo ga kowace ‘yar wasan tawagar Nijeriya ta ƙwallon kwando ta mata, wato D’Tigress. Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ayyana kyautar dala $100,000 da kuma lambar yabo ga duka ‘yan wasan tawagar mata ta ƙwallo...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:20
Shugaban Nijeriya ya ba da kyautar dala $100,000 da lambar yabo ga 'yan wasan D’Tigress
A taƙaice

Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ayyana kyautar dala $100,000 da lambobin yabo ga kowace ‘yar wasan tawagar Nijeriya ta ƙwallon kwando ta mata, wato D’Tigress. Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ayyana kyautar dala $100,000 da kuma lambar yabo ga duka ‘yan wasan tawagar mata ta ƙwallo...

Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ayyana kyautar dala $100,000 da lambobin yabo ga kowace ‘yar wasan tawagar Nijeriya ta ƙwallon kwando ta mata, wato D’Tigress. Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ayyana kyautar dala $100,000 da kuma lambar yabo ga duka ‘yan wasan tawagar mata ta ƙwallon kwando ta ƙasar, wato D’Tigress. Sannan an bai wa kowane jami’an horar da ƙungiyar dala $50,000. Tawagar ce ta lashe gasar ƙwallon kwando ta Afirka, ta 2025, wato FIBA AfroBasket, wanda shi ne karo na biyar a jere da ta samu wannan nasara. Shugaban ya samu wakilcin mataimakinsa, Kashim Shettima a bikin tarbar ‘yan wasan da aka yi a fadar shugaban ƙasa ta Aso Rock da ke birnin Abuja ranar Litinin. Tawagar ƙarƙashin kocin tawagar, Rena Wakama ta samu kyakkyawar tarba daga Kashim Shettima , tare da mai ɗakin shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu, da shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila. A ranar Lahadi ne ‘yan matan suka doke takwarorinsu na Mali da ci 78–64 a gasar da aka kammala a filin wasa na Palais des Sports de Treichville d a ke birnin Abidjan na Ivory Coast. A kwanakin da suka gabata ma Shugaba Tinubu ya yi makamancin wannan kyautar ga ƙungiyar mata ta ƙwallon ƙafa , ta Super Falcons wadda ta lashe kofin Afirka na WAFCON a birnin Rabat na Morocco.