Ana Sayfa / Haber arşivi
Haber arşivi

Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.

Shugaban Majalisar Tarayyar Turai ya yaba da goyon bayan Turkiyya ga Ukraine a yaƙinta da Rasha

‘‘Turkiyya muhimmiyar abokiya ce da ke goyon bayan Ukraine, kuma tana ba da gudumawa a koƙarin majalisar EU na ganin an sasanta,’’ a cewar Antonio Costa. Shugaban Majalisar Tarayyar Turai Antonio Costa ya yaba wa Turkiyya bisa rawar da take takawa wajen nuna goyon bayanta ga Ukraine a yaƙin da ta...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Güncellendi 13.08.2026 05:26:20
Shugaban Majalisar Tarayyar Turai ya yaba da goyon bayan Turkiyya ga Ukraine a yaƙinta da Rasha
Bu haberde ne var?

‘‘Turkiyya muhimmiyar abokiya ce da ke goyon bayan Ukraine, kuma tana ba da gudumawa a koƙarin majalisar EU na ganin an sasanta,’’ a cewar Antonio Costa. Shugaban Majalisar Tarayyar Turai Antonio Costa ya yaba wa Turkiyya bisa rawar da take takawa wajen nuna goyon bayanta ga Ukraine a yaƙin da ta...

‘‘Turkiyya muhimmiyar abokiya ce da ke goyon bayan Ukraine, kuma tana ba da gudumawa a koƙarin majalisar EU na ganin an sasanta,’’ a cewar Antonio Costa. Shugaban Majalisar Tarayyar Turai Antonio Costa ya yaba wa Turkiyya bisa rawar da take takawa wajen nuna goyon bayanta ga Ukraine a yaƙin da take yi da Rasha a ganawar da ya yi da shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a gefen taron babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya kan samar da ƙasashe biyu. Costa ya faɗa a ranar Litinin cewa taron yana da ‘‘muhimmici’’ kuma "Turkiyya babbar abokiya ce da ke goyon bayan Ukraine, wadda ke ba da gudunmawa a ƙoƙarin majalisar EU na ganin an sasanta." Ya ƙara da cewa EU za ta ci gaba da yin aiki tare ƙasar don samun "zaman lafiya mai ɗorewa." ‘‘A shirye mu ke don yin jagoranci a kowane yanki don tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa’’