Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

Shugaban Kenya ya sanya manyan 'yan adawa a jerin ministocinsa

A ranar Laraba ne Ruto ya bayyana sunayen ministoci 10 a jeri na biyu da ya fitar da suka haɗa da ministoci huɗu da atoni janar ɗin da ya sallama daga aiki mako biyu da suka wuce. Shugaban Kenya William Ruto ya sanya sunayen manyan 'yan adawa da kuma wasu ministocin da ya sallama a baya, a jerin...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:20
Shugaban Kenya ya sanya manyan 'yan adawa a jerin ministocinsa
Kwa muhtasari

A ranar Laraba ne Ruto ya bayyana sunayen ministoci 10 a jeri na biyu da ya fitar da suka haɗa da ministoci huɗu da atoni janar ɗin da ya sallama daga aiki mako biyu da suka wuce. Shugaban Kenya William Ruto ya sanya sunayen manyan 'yan adawa da kuma wasu ministocin da ya sallama a baya, a jerin...

A ranar Laraba ne Ruto ya bayyana sunayen ministoci 10 a jeri na biyu da ya fitar da suka haɗa da ministoci huɗu da atoni janar ɗin da ya sallama daga aiki mako biyu da suka wuce. Shugaban Kenya William Ruto ya sanya sunayen manyan 'yan adawa da kuma wasu ministocin da ya sallama a baya, a jerin sabbin ministocin da ya faɗaɗa, bayan zanga-zangar adawa da gwamnati da ta yi sanadin fiye da mutum 50. Shugaban Ƙasar ya ambaci sunan shugaban marasa rinjaye Opiyo Wandayi a matsayin ministan makamashi da ɗan majalisa John Mbadi a matsayin minsitan kuɗi, waɗanda dukkansu 'yan jam'iyyar adawa ta Raila Odinga ce. A ranar Laraba ne Ruto ya bayyana sunayen ministoci 10 a jeri na biyu da ya fitar da suka haɗa da ministoci huɗu da atoni janar ɗin da ya sallama daga aiki mako biyu da suka wuce. A makon da ya wuce ne ya bayyana jerin farko na ministocin. Mambobin Majalisar Dokokin Ƙasar sun amince da sunayen ministocin da Shugaban Ƙasar ya miƙa musu. Ga dai cikakken jerin sunayen ministocin Kenyan da Shugaban Ƙasa ya zaɓa: