Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

Shugaban Kenya William Ruto ya sauke dukkan ministocinsa ban da na Harkokin Ƙasashen Waje

Shugaba William Ruto ya sanar da sauke ministocin daga kan muƙamansu ne a jawabin da ya yi wa 'yan ƙasar ranar Alhamis. Shugaban Kenya William Ruto ya sauke dukkan ministocinsa daga kan muƙamansu ban da na Harkokin Ƙasashen Waje, kwanaki kaɗan bayan an gudanar da jerin zanga-zanga a ƙasar. Shugab...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:20
Shugaban Kenya William Ruto ya sauke dukkan ministocinsa ban da na Harkokin Ƙasashen Waje
Kwa muhtasari

Shugaba William Ruto ya sanar da sauke ministocin daga kan muƙamansu ne a jawabin da ya yi wa 'yan ƙasar ranar Alhamis. Shugaban Kenya William Ruto ya sauke dukkan ministocinsa daga kan muƙamansu ban da na Harkokin Ƙasashen Waje, kwanaki kaɗan bayan an gudanar da jerin zanga-zanga a ƙasar. Shugab...

Shugaba William Ruto ya sanar da sauke ministocin daga kan muƙamansu ne a jawabin da ya yi wa 'yan ƙasar ranar Alhamis. Shugaban Kenya William Ruto ya sauke dukkan ministocinsa daga kan muƙamansu ban da na Harkokin Ƙasashen Waje, kwanaki kaɗan bayan an gudanar da jerin zanga-zanga a ƙasar. Shugaba Ruto ya sanar da sauke ministocin daga kan muƙamansu ne a jawabin da ya yi wa 'yan ƙasar ranar Alhamis. Babu abin da ya shafi Ofishin Mataimakin shugaban ƙasa amma an an sallami antoni janar na ƙasar Ya ce ya ɗauki matakin ne bayan ya yi "tunani, sannan mun saurari abubuwan da 'yan ƙasar Kenya suke buƙata da kuma duba nasarori da ƙalubalen gwamnatina". "Nan-take zan soma tattaunawa da masu ruwa da tsaki a fannoni daban-daban da kuma 'yan siyasa, da zummar kafa gwamnatin da za ta ƙunshi kowa da kowa," in ji shi. Ruto ya ce za a ci gaba da gudanar da harkokin gwamnati ba tare da fuskantar tsaiko ba inda manyan sakatarori da jami'an gwamnati za su jagoranci tafiyar da lamura.