Shugaban Kenya William Ruto ya bayyana zanga-zangar ta ranar Talata a ƙasar a matsayin "cin amanar ƙasa". Shugaban Kenya William Ruto ya bayyana zanga-zangar da aka yi ranar Talata da ta janyo mutuwar mutum biyar da jikkata fiye da mutum 90 a matsayin ‘cin amanar kasa.’ A wani jawabi da ya yi wa ‘yan ƙasa ranar Talata da daddare, Ruto ya ce gwamnati za ta ƙaddamar da martani na gaggawa da zai hukunta “waɗanda suka shirya, da waɗanda suka ɗauki nauyi da masu iza wuta da duk masu hannu a tashin hankali da taɓarɓarewar al’amura.” ‘Yan Kenya daga sassan ƙasar da dama da suka haɗa da babban birnin ƙasar Nairobi, sun yi arangama da ‘yan sanda tsawon yini guda, suna zanga-zangar adawa da ƙarin harajin da suka yi kukan cewa ya yi “yawa” kuma “na rashin imani" ne. Masu zanga-zanga sun kutsa cikin Majalisar Dokokin Kenya Shugaba Ruto yana so ya fito da sabbin haraji kan audugar ƙunzugu ta mata da ake shigar da ita daga waje da wayoyin hannu da babura da kuma sanya haraji kan filayen da aka ware su da sunan wasu tsare-tsare na iyali. Masu zanga-zanga a ƙasar Kenya kan adawa da ƙarin harajin da gwamnati ta yi, sun kutsa kai cikin majalisar dokoki ƙasar. Masu zanga-zangar sun sha alwashin tilasta wa gwamnatin Shugaba William Ruto janye ƙarin harajin, suna masu cewa matakin ya jefa ƙasar cikin bala'i. pic.twitter.com/ajCFObW744 — TRT Afrika Hausa (@trtafrikaHA) June 25, 2024 Kasafin kuɗin da ba a taɓa yin irinsa ba Ruto, wanda ya tsara ƙasafin kuɗin da ya fi duk na baya yawa na kuɗin Kenya shilling tiriliyan 3.9 – ko dala biliyan 30 – na shekarar 2024/2025, ya ce Kenya na buƙatar ƙarin kuɗaɗe, don kauce wa dogaro kan ciyo bashi. Gwamnati ta tura sojoji domin taimaka wa ‘yan sanda domin kawo ƙarshen zanga-zangar.
Arquivo de notícias
Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.
Shugaban Kenya Ruto ya sha alwashin mayar da ‘cikakken martani’ kan zanga-zangar ‘cin amanar ƙasa’
Shugaban Kenya William Ruto ya bayyana zanga-zangar ta ranar Talata a ƙasar a matsayin "cin amanar ƙasa". Shugaban Kenya William Ruto ya bayyana zanga-zangar da aka yi ranar Talata da ta janyo mutuwar mutum biyar da jikkata fiye da mutum 90 a matsayin ‘cin amanar kasa.’ A wani jawabi da ya yi wa...

Em resumo
Shugaban Kenya William Ruto ya bayyana zanga-zangar ta ranar Talata a ƙasar a matsayin "cin amanar ƙasa". Shugaban Kenya William Ruto ya bayyana zanga-zangar da aka yi ranar Talata da ta janyo mutuwar mutum biyar da jikkata fiye da mutum 90 a matsayin ‘cin amanar kasa.’ A wani jawabi da ya yi wa...
