Shugaban Turkiyya na shirin tattaunawa da shugaban Hamas wanda ya isa Istanbul game da yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza a yayin da alƙaluman Falasɗinawan da aka kashe ke ci gaba da ƙaruwa. Shugaban ƙungiyar Hamas da ke fafutukar kare ƴancin Falasɗinawa Ismail Haniyeh ya isa Istanbul domin tattaunawa da shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a yayin da alƙaluman mutanen da Isra'ila ta kashe a yaƙin da take yi a Gaza ya zarta 34,000. Wata sanarwa da Hamas ta fitar ranar Juma'a ta ce Shugaba Erdogan da Haniyeh za su tattauna kan yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, inda ta ƙara da cewa shugaban ya isa ƙasar ce tare da wata tawaga. Lamari na ci gaba da dagulewa a yankin Gabas ta Tsakiya sakamakon harin da Isra'ila ta kai Iran da kuma shirin da take sake yi na ƙaddamar da sabbin hare-hare a Gaza. Ranar Laraba Shugaba Erdogan ya jaddada cewa zai ci gaba da "kare Falasɗinawa kan fafutukar da suke yi kuma mu ci gaba da kasancewa murya ga Falasɗinawa da aka tauye wa hakkinsu". Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya je Qatar ranar Laraba kuma ya ce ya kwashe awanni uku tare da Haniyah da masu ba shi shawara inda suka yi "musayar bayanai kan batutuwa daban-daban musamman game da yarjejeniyar tsagaita wuta".
Архив новостей
В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.
Shugaban Hamas Ismail Haniyeh ya isa Istanbul don tattaunawa da Shugaba Erdogan
Shugaban Turkiyya na shirin tattaunawa da shugaban Hamas wanda ya isa Istanbul game da yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza a yayin da alƙaluman Falasɗinawan da aka kashe ke ci gaba da ƙaruwa. Shugaban ƙungiyar Hamas da ke fafutukar kare ƴancin Falasɗinawa Ismail Haniyeh ya isa Istanbul domin tattaun...

Кратко
Shugaban Turkiyya na shirin tattaunawa da shugaban Hamas wanda ya isa Istanbul game da yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza a yayin da alƙaluman Falasɗinawan da aka kashe ke ci gaba da ƙaruwa. Shugaban ƙungiyar Hamas da ke fafutukar kare ƴancin Falasɗinawa Ismail Haniyeh ya isa Istanbul domin tattaun...
