Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

Shugaban gwamnatin Sudan al-Burhan ya naɗa Al-Haj a matsayin Firaminista

Kazalika Al-Burhan, wanda shi ne shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya, ya naɗa fitaccen jami’in diflomasiyya Omer Mohamed Ahmed Siddiq a matsayin ministan harkokin wajen Sudan. Shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya ta Sudan Abdel Fattah Al-Burhan ya naɗa Dafallah Al-Haj Ali a matsayin firaminista na riƙon ƙ...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:20
Shugaban gwamnatin Sudan al-Burhan ya naɗa Al-Haj a matsayin Firaminista
Kwa muhtasari

Kazalika Al-Burhan, wanda shi ne shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya, ya naɗa fitaccen jami’in diflomasiyya Omer Mohamed Ahmed Siddiq a matsayin ministan harkokin wajen Sudan. Shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya ta Sudan Abdel Fattah Al-Burhan ya naɗa Dafallah Al-Haj Ali a matsayin firaminista na riƙon ƙ...

Kazalika Al-Burhan, wanda shi ne shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya, ya naɗa fitaccen jami’in diflomasiyya Omer Mohamed Ahmed Siddiq a matsayin ministan harkokin wajen Sudan. Shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya ta Sudan Abdel Fattah Al-Burhan ya naɗa Dafallah Al-Haj Ali a matsayin firaminista na riƙon ƙwarya kuma ministan majalisar gudanarwa ta ƙasar . Al-Burhan ya bayyana haka ne a sanarwar da gwamnatinsa ta fitar ranar Laraba da maraice. A halin yanzu Al-Haj shi ne jakadan Sudan a ƙasar Saudiyya kuma tun a shekarar 1980 yake aiki a Ma’aikatar Harkokin Wajen ƙasar. Ya riƙe muƙamin jakadan Sudan a Pakistan, Fadar Vatican da Faransa, sannan shi ne wakilin dindindin na ƙasarsa a Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Musulmai wato Organization of Islamic Cooperation (OIC) da Majalisar Ɗinkin Duniya. Ba a naɗa kowa a matsayin firaminsta ba tun bayan da tsohon firaminista Abdalla Hamdok ya sauka daga kan muƙamin a watan Janairu na shekarar 2022 bayan juyin mulkin da Al-Burhan ya jagoranta a watan Oktoba na 2021. Kazalika Al-Burhan ya naɗa fitaccen jami’in diflomasiyya Omer Mohamed Ahmed Siddiq a matsayin ministan harkokin wajen Sudan da Dr. al-Tahami al-Zein Hajar Mohamed a matsayin Ministan Ma’aikatar Ilimi.