Shugaban mulkin sojin Burkina Faso Kyaftin Ibrahim Traore ya kori Firaministan ƙasar Apollinaire Joachim Kyelem de Tambela da kuma rusa gwamnatin ƙasar kamar yadda babban sakataren gwamnatin ƙasar ya karanto sanarwa a talabijin ɗin ƙasar. Shugaban mulkin sojin Burkina Faso Kyaftin Ibrahim Traore ya kori Firaministan ƙasar Apollinaire Joachim Kyelem de Tambela da kuma rusa gwamnatin ƙasar kamar yadda aka karanto a wata sanarwa a talabijin ɗin ƙasar a ranar Juma’a da dare. Sanarwar ta bayyana cewa “mambobin gwamnatin da aka sauke za su ci gaba da gudanar da ayyukansu har sai an kafa sabuwar gwamnati.” Matias Traoré, wanda shi ne babban sakataren gwamnati da kuma majalisar ministoci shi ne ya karantar sanarwar a talabijin. A Mali ma an samu irin haka inda a ranar 11 ga watan Nuwamba Janar Assimi Goita ya sallami Firaminista Choguel Kokalla Maiga kwanaki bayan firaministan ya caccaki gwamnatin ƙasar. Burkina Faso da Mali da Nijar sun kafa ƙungiyar haɗaka mai suna Sahel Alliance a Satumnbar 2023 tare da sanar da kafa ƙungiya ta musamman ta soji wadda za ta yaƙi ‘yan ta’addan da suka addabi yankin.
Taskar labarai
Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.
Shugaban Burkina Faso Traore ya sallami Firaministan ƙasar Apollinaire Kyelem
Shugaban mulkin sojin Burkina Faso Kyaftin Ibrahim Traore ya kori Firaministan ƙasar Apollinaire Joachim Kyelem de Tambela da kuma rusa gwamnatin ƙasar kamar yadda babban sakataren gwamnatin ƙasar ya karanto sanarwa a talabijin ɗin ƙasar. Shugaban mulkin sojin Burkina Faso Kyaftin Ibrahim Traore...

A taƙaice