الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

Shugaba Tinubu ya tafi Faransa da Ingila don fara hutun shekara-shekara na kwana 10

A watan Oktoban shekarar 2024 ma shugaban na Nijeriya ya tafi hutun shekara-shekara na mako biyu. Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya fara hutun shekara-shekara ranar Alhamis 4 ga watan Satumba na wannan shekarar. Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Nijeriya, Bayo Onanuga, ya wallaf...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:20 ص
Shugaba Tinubu ya tafi Faransa da Ingila don fara hutun shekara-shekara na kwana 10
لمحة سريعة

A watan Oktoban shekarar 2024 ma shugaban na Nijeriya ya tafi hutun shekara-shekara na mako biyu. Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya fara hutun shekara-shekara ranar Alhamis 4 ga watan Satumba na wannan shekarar. Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Nijeriya, Bayo Onanuga, ya wallaf...

A watan Oktoban shekarar 2024 ma shugaban na Nijeriya ya tafi hutun shekara-shekara na mako biyu. Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya fara hutun shekara-shekara ranar Alhamis 4 ga watan Satumba na wannan shekarar. Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Nijeriya, Bayo Onanuga, ya wallafa a shafinsa na X, ta ce shugaban zai shafe kwanakin aiki goma yana hutun na shekara-shekara. “Shugaba Tinubu zai yi hutun ne tsakanin Faransa da Birtaniya kana ya dawo ƙasar [Nijeriya],” in ji sanarwar. Daga bisani shugaban na Nijeriya ya tashi daga Abuja inda ya nufi Turai a jirgin shugaban ƙasa.