Za a gudanar da ziyarar ƙasa ta yini biyu a watan Maris Sarkin Charles na uku na Birtaniya zai karɓi baƙuncin Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu, a wata ziyarar ƙasa da ƙasa ta yini biyu da za a yi a ranakun 18–19 ga Maris, kamar yadda Fadar Buckingham ta bayyana a ranar Asabar. TRT Hausa Za a tarbi Shugaba Tinubu da uwargidansa Oluremi Tinubu a Fadar Windsor da ke yammacin London, inda Sarki Charles da Sarauniya Camilla za su karɓe su a hukumance. TRT Hausa Ziyarar na zuwa ne bayan da Birtaniya da Nijeriya suka ƙulla kawancen dabaru a watan Nuwamban 2024 domin ƙarfafa haɗin gwiwa a fannoni irin su tattalin arziki, shige da fice da tsaro. TRT Hausa Ma’aikatar Tsaron Nijeriya ta ce ƙasashen biyu na shirin ƙara zurfafa haɗin gwiwar tsaro, musamman bayan kisan fiye da mutane 160 a Jihar Kwara da Shugaba Tinubu ya danganta da ayyukan ta’addanci. TRT Hausa Wannan ita ce ziyarar ƙasa ta farko a hukumance daga shugaban Nijeriya zuwa Birtaniya cikin shekaru 37, duk da cewa Sarki Charles ya ziyarci Nijeriya sau huɗu a baya a lokacin da yake Yarima na Wales. TRT Hausa
Arquivo de notícias
Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.
Sarki Charles zai karɓi baƙuncin Tinubu a Birtaniya
Za a gudanar da ziyarar ƙasa ta yini biyu a watan Maris Sarkin Charles na uku na Birtaniya zai karɓi baƙuncin Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu, a wata ziyarar ƙasa da ƙasa ta yini biyu da za a yi a ranakun 18–19 ga Maris, kamar yadda Fadar Buckingham ta bayyana a ranar Asabar. TRT Hausa Za a tarbi...

Em resumo