Início / Arquivo de notícias
Arquivo de notícias

Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.

Shugaba Erdogan ya sha alwashin taimaka wa waɗanda girgizar ƙasa ta shafa a watan Fabrairun 2023 a Turkiyya

A yayin tunawa da zagayowar ranar farko ta munanan girgizar ƙasa, Recep Tayyip Erdogan ya ce "irin waɗannan manyan bala'o'i suna koya juriya ga mutanen da ke gwada ƙarfin haɗin kai da 'yan'uwantaka". Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi alƙawarin faranta rayukan waɗanda girgizar ƙas...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Atualizado 13/08/2026, 05:26:20
Shugaba Erdogan ya sha alwashin taimaka wa waɗanda girgizar ƙasa ta shafa a watan Fabrairun 2023 a Turkiyya
Em resumo

A yayin tunawa da zagayowar ranar farko ta munanan girgizar ƙasa, Recep Tayyip Erdogan ya ce "irin waɗannan manyan bala'o'i suna koya juriya ga mutanen da ke gwada ƙarfin haɗin kai da 'yan'uwantaka". Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi alƙawarin faranta rayukan waɗanda girgizar ƙas...

A yayin tunawa da zagayowar ranar farko ta munanan girgizar ƙasa, Recep Tayyip Erdogan ya ce "irin waɗannan manyan bala'o'i suna koya juriya ga mutanen da ke gwada ƙarfin haɗin kai da 'yan'uwantaka". Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi alƙawarin faranta rayukan waɗanda girgizar ƙasar da ta afku a yankin kudancin ƙasar a ranar 6 ga watan Fabrairun 2023 ta shafa. "Zafin rayukan da muka rasa a girgizar ƙasar da ta faru wacce ta fi muni a Kahramanmaras, wacce muka fuskanta shekara guda da ta wuce, na ci gaba da ƙona zukatanmu tamkar yau abin ya faru," in ji Erdogan a yayin tunawa da ranar farko ta girgizar ƙasa mai ƙarfin gaske da ta kashe mutum 53,537 tare da jikkata wasu fiye da 107,000. Bir yıl önce yaşadığımız Kahramanmaraş merkezli depremlerde kaybettiğimiz canların acısı ilk günkü tazeliğiyle yüreklerimizi yakmayı sürdürüyor. Yitirdiğimiz 53 bin 537 canımızın her birine Allah’tan rahmet, yakınlarına ve milletimize başsağlığı diliyorum.… pic.twitter.com/19AufD6qMt — Recep Tayyip Erdoğan (@RTErdogan) February 6, 2024 'Bala'in ƙarni' Ɓarnar da aka samu a larduna 11, waɗanda ke cikin tsofaffin matsugunai a tarihin ɗan'adam, "ta yi girma ƙwarai da gaske," in ji Shugaban. Girgizar ƙasa masu ƙarfin maki 7.7 da 7.6 sun afku ne a larduna 11 na Turkiyya - Adana da Adiyaman da Diyarbakir da Elazig da Hatay da Gaziantep da Kahramanmaras da Kilis da Malatya da Osmaniye da Sanliurfa. Fiye da mutum miliyan 13.5 ne girgizar kasar ta shafa a Turkiyya, da kuma wasu da dama a arewacin Siriya. Edogan ya kara da cewa, irin waɗannan manyan bala'o'i da wahalhalun da ake fuskanta, matsaloli ne da suke koyar da jajircewa a inda ake gwada ƙarfin haɗin kai da 'yan'uwantaka, inda ya ƙara da cewa, al'ummar ƙasar sun yi nasara a kan wannan jarrabawa mai raɗaɗi a tarihi. Yayin da gwamnatin kasar ta dauki matakin gaggawa da dukkan ƙarfinta, Erdogan ya ce, Turkiyya ta hada kai wajen yaƙi da bala'in ƙarni. Shugaban ya kuma jaddada cewa gwamnati na aiki tuƙuru domin ganin ta cika alkawuran da ta yi wa al’ummar ƙasar, shugaban ya ƙara da cewa, “Za mu ci gaba da wannan ƙoƙari har sai mun gina da kuma farfaɗo da garuruwanmu.