Mutane da dama ciki har da wadanda suke goyon bayan gwamnati sun nuna adawarsu da shirin Gwamna Abba Kabir Yusuf na gina sabuwar gada a unguwar Dan-Agundi suna masu cewa akwai abubuwan da suka fi ta muhimmanci. Matakin da gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ta dauka na yin amfani da kudaden kananan hukumomi wurin gina wata gada a cikin birnin Kano ya jawo wa Gwamna Abba Kabir Yusuf suka. Gwamnatin ta jihar Kano, a wata takarda da ofishin Babban Akanta na Jihar ya fitar, ta amince a kashe kusan Naira biliyan goma sha shida domin gina gadar kasa da ta sama a unguwar Dan-Agundi da ke cikin birnin Kano. Za a yi hadin gwiwa tsakanin gwamnatin jiha da gwamnatocin kananan hukumomi wurin gina gadar inda jiha za ta bayar da kashi 30 yayin da kananan hukumomi za su bayar da kashi 70, in ji takardar. "Don haka Majalisar Zartarwa ta jiha ta amince a fitar da naira biliyan shida da miliyan dari uku da tamanin da tara" a matsayin kudin kafin-alkalami ga dan kwangilar da zai yi wannan aiki, in ji gwamnatin. Sai dai tuni wannan mataki ya soma fuskantar suka daga wadanda suke gani bai kamata a yi amfani da kudin kananan hukumomi wurin gudanar da irin wannan aiki a cikin birni ba bayan kuwa su ne suka fi cancanta wurin samun ayyukan ci-gaba. A gefe guda, wasu suna ganin gina gada a wannan lokaci da talakawa ke bukatar ayyukan wajibi kamar samar da ruwan sha da gina asibitoci da makarantu da sauransu, ba shi ne ya zama abu mafi muhimmanci ba. Fitaccen lauyan nan na jihar Kano, Abba Hikima, ya yi tsokaci a kan hakan inda ya ce "Don Allah a tsayar da wannan aikin. Irin wadannan abubuwan ne suke sa wa mutane suke dauka gaba daya ashe 'yan siyasa irinsu daya. Yanzu saboda Allah ina adalci a nan? Kauyukan Kano suna cikin mawuyacin hali... amma a dauko kudin su a saka a gada guda daya? Me wannan kudin?" A baya dai, jami'an gwamnati mai ci sun rika sukar gwamnatin tsohon Gwaman Abdullahi Ganduje kan gina gadoji, shi ya sa ma wasu a wannan karon suke sukarsu bisa shirin gina gadar ta Dan-Agundi. Malam Abdul Aziz Abdul Aziz, mai taimaka wa shugaban Nijeriya kan watsa labarai, ya ce "Lokacin da na ga sanarwar gina waɗannan gadoji na yi wa wasu abokai na guda biyu personal message (saboda gudun magana publicly ƴan baka su maida abin siyasa). "Abin da na rubuta musu shi ne idan har mun ta sukar Ganduje a kan wajen kashe maƙudan kuɗaɗe don gina gadoji alhali akwai bukatu na gaggawa ban ga dalilin yin shiru a kan gadar Tal'udu da sauran da Abba yake shirin yi ba."
Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.
Shirin gwamnatin Kano na gina sabuwar gada a Dan-Agundi ya tayar da kura
Mutane da dama ciki har da wadanda suke goyon bayan gwamnati sun nuna adawarsu da shirin Gwamna Abba Kabir Yusuf na gina sabuwar gada a unguwar Dan-Agundi suna masu cewa akwai abubuwan da suka fi ta muhimmanci. Matakin da gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ta dauka na yin amfani da kuda...

Mutane da dama ciki har da wadanda suke goyon bayan gwamnati sun nuna adawarsu da shirin Gwamna Abba Kabir Yusuf na gina sabuwar gada a unguwar Dan-Agundi suna masu cewa akwai abubuwan da suka fi ta muhimmanci. Matakin da gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ta dauka na yin amfani da kuda...
