Главная / Архив новостей
Архив новостей

В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.

Shawo kan rikicin Gaza babban nauyi ne da ya rataya a wuyan duniya: Hakan Fidan

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya bayyana cewa wasu ƙasashen duniya suna toshe kunnunwansu idan ana magana kan hare-haren da Isra'ila kai kaiwa a Gaza Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya jaddada muhimmancin tsagaita wuta mai ɗorewa a Gaza da ke Falasɗinu, inda ya yi kira...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Обновлено 13.08.2026, 05:26:20
Shawo kan rikicin Gaza babban nauyi ne da ya rataya a wuyan duniya: Hakan Fidan
Кратко

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya bayyana cewa wasu ƙasashen duniya suna toshe kunnunwansu idan ana magana kan hare-haren da Isra'ila kai kaiwa a Gaza Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya jaddada muhimmancin tsagaita wuta mai ɗorewa a Gaza da ke Falasɗinu, inda ya yi kira...

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya bayyana cewa wasu ƙasashen duniya suna toshe kunnunwansu idan ana magana kan hare-haren da Isra'ila kai kaiwa a Gaza Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya jaddada muhimmancin tsagaita wuta mai ɗorewa a Gaza da ke Falasɗinu, inda ya yi kira da a soma tattaunawa kan batun samar da ƙasa biyu wato two-state solution tsakanin Falasɗinu da Isra’ila. Ya zama wani haƙƙi mai muhimmanci wajen a kawo ƙarshen wannan babban bala'i da kisan kiyashi da ake yi wa 'yan'uwanmu na Gaza cikin gaggawa tare da tabbatar da cewa an dauki kwararan matakai don kawo karshen wannan lamari,” kamar yadda Fidan ya shaida wa manema labarai na ƙasar Turkiyya a Washington a ranar Juma’a. Fidan yana ziyara ta kwana biyu a Amurka domin tattaunawa da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken don tattaunawa kan dangantaka tsakanin ƙasashe da harkokin waje musamman halin da ake ciki a Gaza. An haɗa wani taron tsakanin Turkiyya da Amurka a lokacin ziyarar tasa inda Fidan ɗin ya haɗu da manyan jami’an Amurka daga ciki har da Babban Mai Ba Shugaban Amurka Shawara Kan Harkokin Tsaro Jake Sullivan da Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawan Amurka Kan Harkokin Waje Benjamin Cardin da kuma Phil Gordon wanda shi ne Babban Mai Ba Mataimakiyar Shugaban Amurka Shawara Kan Harkokin Tsaro Kamala Harris. Fidan ya bayyana cewa Turkiyya na son a duba yiwuwar kai agajin jin kai cikin gaggawa ga jama’ar Gaza. “Ba a taɓa cimma yarjejeniya irin wannan ba a ko wane irin taro a duniya ba,” in ji Fidan inda ya ƙara da cewa ƙasashe irin su Turkiyya na son a samar da yarjejeniyar tsagaita wuta maras cikas. Ƙasashen da ke zama 'kurame da makafi' dangane da Isra'ila Fidan ya ce kungiyoyin kasa da kasa, musamman ma MDD, da kasashe da dama na ganin wajibi ne su yi wani abu game da halin da ake ciki na jin kai a Gaza. Ya ce matakin da Amurka ta dauka na kafa tashar ruwa ta wucin gadi a Gaza domin samun agaji ya biyo bayan martanin da kasashen duniya suka mayar. Ministan ya ƙara da cewa wasu ƙasashen suna kasancewa tamkar “makafi da kurame” idan ana magana kan abubuwan da Isra’ila ke aikatawa. “Kisan farar hula sama da 30,000 a Gaza da gangan, alama ce ta wani mataki na zalunci,” in ji shi, haka kuma ci gaba da wannan rikicin “lamari ne da ba za a iya jure masa ba.” Isra'ila ta kaddamar da wani gagarumin yakin soji a Gaza a matsayin martani ga harin da kungiyar Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda Tel Aviv ta ce ya kashe mutane aƙalla 1,200.