Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

Sarkin Kuwait Nawaf al-Ahmad al-Sabah ya rasu

Al-Sabah ya rasu da safiyar Asabar bayan an kai shi asibiti sakamakon rashin lafiyar da yake fama da ita, kamar yadda rahotanni suka tabbatar. Sarkin Kuwait Sheikh Nawaf al-Ahmad al-Sabah ya rasu a ranar Asabar da safe. Ministan Harkokin Masarautar Kuwait Mohammad Abdullah Al-Mubarak Al-Sabah ya...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:20
Sarkin Kuwait Nawaf al-Ahmad al-Sabah ya rasu
De un vistazo

Al-Sabah ya rasu da safiyar Asabar bayan an kai shi asibiti sakamakon rashin lafiyar da yake fama da ita, kamar yadda rahotanni suka tabbatar. Sarkin Kuwait Sheikh Nawaf al-Ahmad al-Sabah ya rasu a ranar Asabar da safe. Ministan Harkokin Masarautar Kuwait Mohammad Abdullah Al-Mubarak Al-Sabah ya...

Al-Sabah ya rasu da safiyar Asabar bayan an kai shi asibiti sakamakon rashin lafiyar da yake fama da ita, kamar yadda rahotanni suka tabbatar. Sarkin Kuwait Sheikh Nawaf al-Ahmad al-Sabah ya rasu a ranar Asabar da safe. Ministan Harkokin Masarautar Kuwait Mohammad Abdullah Al-Mubarak Al-Sabah ya ce sarkin ya rasu yana da shekara 86 da haihuwa. A cewarsa, an kai sarkin asibiti da safe sakamakon bukatar gaggawa amma daga baya Allah ya yi masa rasuwa, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Kuwait ya ruwaito. Ya bayyana cewa ko a watan da ya gabata sai da aka kai sarkin asibiti sakamakon rashin lafiyar da yake fama da ita. Sheikh Nawaf ya zama yarima mai jiran gado a 2006, bayan dan uwansa Sheikh Sabah al-Ahmad Al-Sabah ya nada shi. Ya zama Sarkin Kuwait bayan rasuwar dan uwan nasa a Satumbar 2020 a lokacin da yake da shekara 91 da haihuwa. A halin yanzu Sheikh Mishal al-Ahmad al-Sabah mai shekara 83 shi ne yarima mai jiran gado na kasar