Sanarwar ta ambato Kwamishinan 'Yan sandan Kano Mohammed Usaini Gumel yana cewa za su ba da tsaro ga Alhaji Aminu Ado Bayero domin ya yi Sallar Juma'a a masallacin da ke Fadar Sarki ta Nasarawa inda yake zaune. Rundunar 'yan sandan Nijeriya reshen jihar Kano ta ƙaryata rahotannin da ke cewa Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero zai jagoranci Sallar Juma'a a Masallacin Kofar Kudu da ke cikin Birni. Ta bayyana haka ne a wata sanarwa da kakakin Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ranar Juma'a da safe. "Rundunar 'yan sanda reshen Jihar Kano tana mai umartar dukkan mutane su yi watsi da labaran ƙarya da ake watsawa a soshiyal midiya cewa Sarki Alhaji Aminu Ado Bayero zai jagoranci Sallar Jumma’t a Babban Masallaci da ke Ƙofar Kudu, Kano," in ji sanarwar. Gwamnan Kano ya ba da umarnin kama Aminu Ado Bayero Sai dai sanarwar ta ambato Kwamishinan 'yan sanda na Jihar Mohammed Usaini Gumel yana mai tabbatar da cewa sun ɗauki dukkan matakan tsaro da za su bai wa Alhaji Aminu Ado Bayero domin ya yi Sallar Juma'a a masallacin da ke Fadar Sarki ta Nasarawa inda yake zaune.
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
Sarki Aminu Ado Bayero ba zai jagoranci Sallar Juma'a ba - Rundunar 'yan sandan Kano
Sanarwar ta ambato Kwamishinan 'Yan sandan Kano Mohammed Usaini Gumel yana cewa za su ba da tsaro ga Alhaji Aminu Ado Bayero domin ya yi Sallar Juma'a a masallacin da ke Fadar Sarki ta Nasarawa inda yake zaune. Rundunar 'yan sandan Nijeriya reshen jihar Kano ta ƙaryata rahotannin da ke cewa Sarki...

At a glance