Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

Sabon rikici ya barke tsakanin sojin Sudan da dakarun RSF

Tun da farko RSF ta yi ikirarin kwace fadar shugaban kasar da wasu muhimman wurare. Sai dai rundunar soji ta musanta wannan batu. Sabon rikici ya barke tsakanin sojojin Sudan da dakarun rundunar tsaro ta Rapid Support Forces sa'o'i bayan sun amince su tsagaita wuta. Rahotanni sun nuna cewa an ji...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:20
Sabon rikici ya barke tsakanin sojin Sudan da dakarun RSF
Kwa muhtasari

Tun da farko RSF ta yi ikirarin kwace fadar shugaban kasar da wasu muhimman wurare. Sai dai rundunar soji ta musanta wannan batu. Sabon rikici ya barke tsakanin sojojin Sudan da dakarun rundunar tsaro ta Rapid Support Forces sa'o'i bayan sun amince su tsagaita wuta. Rahotanni sun nuna cewa an ji...

Tun da farko RSF ta yi ikirarin kwace fadar shugaban kasar da wasu muhimman wurare. Sai dai rundunar soji ta musanta wannan batu. Sabon rikici ya barke tsakanin sojojin Sudan da dakarun rundunar tsaro ta Rapid Support Forces sa'o'i bayan sun amince su tsagaita wuta. Rahotanni sun nuna cewa an ji karar makaman atilari a yankuna daban-daban na Khartoum, babban birnin Sudan ranar Lahadi duk da tsagaita wutar da bangarorin biyu suka yi. Da ma dai bangarori biyu sun tsagaita wuta ne domin a samu damar kai "agajin gaggawa" da kuma fitar da mutane daga yankunan da lamarin ya shafa. Da farko wakilan sojin kasa ta Sudan da na RSF sun amince da tayin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi na tsagaita wuta daga karfe hudu zuwa karfe bakwai na yamma a agogon kasar. Janar Burhan na rundunar sojin kasa ta Sudan da Janar Mohamed Hamdan Dagalo Rapid Support Forces sun amince da wannan tsari. An kwashe ranar Asabar zuwa wani bangare na Lahadi ana gumurzu tsakanin sojin Sudan da rundunar tsaro ta musamman mai karfin iko RSF a Khartoum da wasu yankunan kasar, lamarin da ya jefa tsananin tsoro a zukatan 'yan kasar. Kungiyar likitoci ta Sudan ta ce kawo yanzu an kashe mutum 56 sakamakon arangamar da aka yi tsakanin sojojin kasar da dakarun rundunar tsaro ta musamman. Ta ce akalla mutum 600 sun jikkata sakamakon lamarin. Mutanen da suka mutu sun hada da ma'aikatan Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya guda uku. Shugaban Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi tir da rikicin da ke faruwa a Sudan yana mai kira a tabbatar da adalci kan kashe-kashen da aka yi. A jerin sanarwar da ta fita RSF ta yi ikirarin kwace fadar shugaban kasar da wasu muhimman wurare. Ta ce ta "kwace cikakken iko" na fadar shugaban kasar da filin jirgin saman Khartoum da na Merowe da ke arewacin kasar. Sai dai rundunar sojin Sudan ta ce ita ke da rike da dukkan wuraren da dakarun RSF suka yi ikirarin kwacewa. Jiragen yakin Sudan sun kai hare-hare kan sansanonin RSF da ke Khartoum, a cewar rundunar sojin, inda ta karawa da cewa sojoji sun kai farmaki kan mayakan RSF kuma ta umarci fararen hula su zauna a gidajensu. Kasashen duniya sun bayyana damuwarsu game da abin da ke faruwa a Sudan, suna kira ga bangarorin da su yi sulhu. Ma'aikatar wajen Turkiyya ta ce "mun damu da arangamar da ake yi tsakanin" bangarorin biyu tana mai kira da su tabbatar da tsarin mayar da mulki hannun farar hula. Ta kara da cewa "Turkiyya za ta cigaba da kasancewa kawa ga Sudan." Tsoho Firaiministan Sudan Abdallah Hamdok ya bukaci a "tsagaita wuta nan take" sannan ya yi kira ga al'ummar kasar su "jajirce". Bangarorin biyu suna tayar da jijiyoyin wuya ne game da wa'adin mika mulkin kasar ga gwamnatin farar hula. Sai dai kafin nan shugaban mulkin soji na Sudan Janar Abdel Fattah al Burhan ya ce a shirye yake ya kawo karshen rashin jituwa tsakaninsu da RSF. Wata sanarwa da masu shiga tsakani domin sasanta bangarorin biyu ce ta bayyana hakan ranar Asabar. “Muna tabbatar wa jama’ar kasa cewa ana kan hanyar kawo karshen wannan rikici,” in ji sanarwar. Titunan Khartoum sun kasance kusan fayau ranar Asabar. (AFP) Zaman dar-dar ya karu tsakanin sojojin Sudan da RSF a ranar Alhamis bayan da rundunar ta mayar da sojojinta kusa da filin jirgin saman soji da ke birnin Merowe, abin da rundunar sojin kasar ta ce an yi shi ba tare da yardar ta ba. Daga nan ne sojojin suka yi gargadi kan yiwuwar fito-na-fito tsakanin bangarorin biyu. Rundunar ta RSF, wadda tare da ita aka hada kai wajen kifar da gwamnatin Omar al Bashir a 2019, ta soma tura dakarunta Khartoum da wasu wurare a lokacin da ake tattaunawa a watan jiya kan mayar da ita cikin soji. Wannan rashin jituwar ta kawo jinkiri wurin saka hannu kan yarjejeniya ta karshe tsakanin jam’iyyun siyasa da kuma kafa gwamnatin farar hula. Bayan gargadin da sojin suka yi a ranar Alhamis, kungiyoyi da dama daga ciki da wajen Sudan suka fito domin shiga tsakani daga ciki har da ministan kudi na kasar Jibril Ibrahim da Gwamnan Darfur Minni Minawi da mamba a gwamnatin rikon kwarya ta kasar Malik Agar. Sauran sun hada da tsofaffin shugabannin ‘yan tawaye uku wadanda aka ba su mukami bayan yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi da su a 2020. 'Babu kasa mai rundunar soji biyu' Batun yin fito-na-fito da kuma yadda ake ganin motocin sulke da na soji a Khartoum ya sa jama’a suka shiga cikin zulumi, kamar yadda jama’a da dama suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters. Da dama sun dora alhakin hakan kan duka bangarorin biyu. “Suna rikici kan mulki da jefa kasa cikin wani hali, mu kuma muna fafutukar samun abinci da abin sha da ilimi da kiwon lafiya,” in ji Nafisa Suleiman, yayin da take a wani wuri da ake sayar da kayan lambu. “Ya kamata sojoji su rinka kare mutane amma a yanzu sun ne babbar barazana,” in ji wani mai shekara 35 Isam Hassan. “Ya kamata RSF ta zama karkashin soji. Babu kasar da ke da rundunar soji biyu,” kamar yadda ya kara da cewa.