Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

Sabon karnin Jamhuriya zai zama shi ne Karnin Turkiyya: Altun

Daraktan Sadarwar Fahrettin Altun ya ce taimakon jinƙai da matsayar siyasa da Shugaba Tayyip Erdogan ke jagoranta a kan lamarin Isra'ila da Falasdinu a baya-bayan nan sun tabbatar da ƙoƙrin Turkiyya da iyawarta a kan al'amuran duniya. Ana girmama Turkiyya a ƙasashen duniya kuma tana samun nasara...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:20
Sabon karnin Jamhuriya zai zama shi ne Karnin Turkiyya: Altun
Kwa muhtasari

Daraktan Sadarwar Fahrettin Altun ya ce taimakon jinƙai da matsayar siyasa da Shugaba Tayyip Erdogan ke jagoranta a kan lamarin Isra'ila da Falasdinu a baya-bayan nan sun tabbatar da ƙoƙrin Turkiyya da iyawarta a kan al'amuran duniya. Ana girmama Turkiyya a ƙasashen duniya kuma tana samun nasara...

Daraktan Sadarwar Fahrettin Altun ya ce taimakon jinƙai da matsayar siyasa da Shugaba Tayyip Erdogan ke jagoranta a kan lamarin Isra'ila da Falasdinu a baya-bayan nan sun tabbatar da ƙoƙrin Turkiyya da iyawarta a kan al'amuran duniya. Ana girmama Turkiyya a ƙasashen duniya kuma tana samun nasara a muhimmiyar rawar da take takawa, musamman a kan al'amuran da suka shafi yankin, ciki har da lamarin Gabas ta Tsakiya da kafatanin yankin Asiya, in ji daraktan sadarwa na ƙasar. A wata maƙala da aka wallafa a Jaridar Daily Express ta Birtaniya da Interfax ta Rasha, Daraktan Sadarwar Fahrettin Altun ya ce taimakon jinƙai da matsayar siyasa da Shugaba Tayyip Erdogan ke jagoranta a kan lamarin Isra'ila da Falasdinu a baya-bayan nan sun tabbatar da ƙoƙrin Turkiyya da iyawarta a kan al'amuran duniya. "Kamar yadda aka gani a kan sha'anin Ukraine da Karabakh da sauran al'amuran da suka shafi yankin, a yayin da muke shiga ƙarni na biyu na zamowar Turkiyya Jamhuriyar, ƙasar ta zamo wata mai faɗa a ji a yankin," in ji Altun.