Accueil / Archives
Archives

Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.

Rwanda ta tabbatar da ɓullar cutar Marburg a karon farko a ƙasar

Cutar Marburg na saka zazzaɓi mai ƙarfi tare da yaɗuwa a tsakanin mutane, kamar dai yadda cutar Ebola take, in ji WHO. Rwanda ta sanar da samun ɓullar cutar Marburg a karon farko a ƙasar, inda mutane takwas suka mutu bayan kamuwa da ita, in ji Ma'aikatar Lafiya a ranar Lahadi. Ya zuwa 29 ga Satum...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Mis à jour 13/08/2026 05:26:20
Rwanda ta tabbatar da ɓullar cutar Marburg a karon farko a ƙasar
En bref

Cutar Marburg na saka zazzaɓi mai ƙarfi tare da yaɗuwa a tsakanin mutane, kamar dai yadda cutar Ebola take, in ji WHO. Rwanda ta sanar da samun ɓullar cutar Marburg a karon farko a ƙasar, inda mutane takwas suka mutu bayan kamuwa da ita, in ji Ma'aikatar Lafiya a ranar Lahadi. Ya zuwa 29 ga Satum...

Cutar Marburg na saka zazzaɓi mai ƙarfi tare da yaɗuwa a tsakanin mutane, kamar dai yadda cutar Ebola take, in ji WHO. Rwanda ta sanar da samun ɓullar cutar Marburg a karon farko a ƙasar, inda mutane takwas suka mutu bayan kamuwa da ita, in ji Ma'aikatar Lafiya a ranar Lahadi. Ya zuwa 29 ga Satumba, an samu mutane 26 ɗauke da cutar a ƙasar da ke Gabashin Afirka, in ji ma'aikatar a sanawar da ta fitar ta shafin X. "Mutane za su iya ci gaba da harkokinsu na yau da kullum - ba a hana gudanar da wani aiki ba a matsayin matakan magance cutar Marburg. Kar mutane su firgita a yayin da muka gano dukkan yankunan da cutar ta bulla kuma ana daukar matakan da suka kamata," in ji Ministan Lafiya na rwanda Sabin Nsanzimana a shafin X. Cutar Marburg na saka zazzabi mai karfi tare da yaduwa a tsakanin mutane, kamar dai yadda cutar Ebola ta ke, in ji Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO). Ana ɗaukar cutar Marburg daga jemagun bishiyun kayan marmari kuma tana yaduwa a tsakanin mutane bayan cudanya da mai dauke da ita, ko taba wani waje da mai cutar ya taba.