Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta yi bayani kan kisan da aka yi wa jami’anta a Borno

“Kwamishinan ‘yan sanda CP MI Yusufu ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan ‘yan sanda hudu da suka rasa rayukansu a yayin da suke kare Unguwar ‘Yan sanda ta Gajiram a Nganzai,” in ji sanarwar. Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta musanta rahotannin da ke cewa an kai hari a Hedkwatarta da ke Maiduguri babban...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:19
Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta yi bayani kan kisan da aka yi wa jami’anta a Borno
A taƙaice

“Kwamishinan ‘yan sanda CP MI Yusufu ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan ‘yan sanda hudu da suka rasa rayukansu a yayin da suke kare Unguwar ‘Yan sanda ta Gajiram a Nganzai,” in ji sanarwar. Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta musanta rahotannin da ke cewa an kai hari a Hedkwatarta da ke Maiduguri babban...

“Kwamishinan ‘yan sanda CP MI Yusufu ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan ‘yan sanda hudu da suka rasa rayukansu a yayin da suke kare Unguwar ‘Yan sanda ta Gajiram a Nganzai,” in ji sanarwar. Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta musanta rahotannin da ke cewa an kai hari a Hedkwatarta da ke Maiduguri babban birnin jihar Borno na arewa maso gabashin kasar. Ta bayyana haka ne a wata sanarwa da mai magana da yawunta na jihar ta Borno ASP Nahum Daso Kenneth ya fitar ranar Asabar da maraice. Kenneth ya ce ba a kai hari a “Hedkwatar rundunar ‘yan sanda ta jiha da ke Maiduguri ba” kuma tana karkashin kulawar jami’an tsaro sannan tana aiki. Sai dai ya kara da cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari a Unguwar ‘Yan sanda da ke “garin Gajiram na karamar hukumar Nganzai” ranar 2 ga watan Fabrairu da tsakar dare lamarin da ya yi sanadin mutuwar wasu dakarunsu. 'Yan sanda sun kama mutumin da ake zargi da kashe matarsa a Borno “Kwamishinan ‘yan sanda CP MI Yusufu ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan ‘yan sanda hudu da suka rasa rayukansu a yayin da suke kare Unguwar ‘Yan sanda ta Gajiram a Nganzai,” in ji sanarwar. Borno na ci gaba da fuskantar hare-hare daga mayakan Boko Haram da na ISWAP wadanda suka kwashe shekaru da dama suna addabar jihar. Mayakan sun kashe dubban mutane tare da raba miliyoyi da gidajensu, baya ga sace mutane ciki har da dalibai.