Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

Rundunar tsaron Nijeriya ta ƙaddamar da bincike kan kashe sojojinta a Jihar Delta

Sojojin waɗanda suka haɗa da kwamanda ɗaya da masu muƙamin manjo guda biyu da kyaftin ɗaya da kuma kuratan sojoji 12 sun rasu ne a yayin da suka kai ɗauki lokacin da ake wani rikicin ƙabilanci. Hedkwatar Tsaron Nijeriya ta ce ta ƙaddamar da gagarumin bincike bayan wasu matasa sun kashe sojojinta...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:19
Rundunar tsaron Nijeriya ta ƙaddamar da bincike kan kashe sojojinta a Jihar Delta
A taƙaice

Sojojin waɗanda suka haɗa da kwamanda ɗaya da masu muƙamin manjo guda biyu da kyaftin ɗaya da kuma kuratan sojoji 12 sun rasu ne a yayin da suka kai ɗauki lokacin da ake wani rikicin ƙabilanci. Hedkwatar Tsaron Nijeriya ta ce ta ƙaddamar da gagarumin bincike bayan wasu matasa sun kashe sojojinta...

Sojojin waɗanda suka haɗa da kwamanda ɗaya da masu muƙamin manjo guda biyu da kyaftin ɗaya da kuma kuratan sojoji 12 sun rasu ne a yayin da suka kai ɗauki lokacin da ake wani rikicin ƙabilanci. Hedkwatar Tsaron Nijeriya ta ce ta ƙaddamar da gagarumin bincike bayan wasu matasa sun kashe sojojinta aƙalla goma sha shida a Jihar Delta da ke kudu maso kudancin ƙasar. Daraktan watsa labarai na sojin ƙasar Birgediya Janar Tukur Gusau ne ya tabbatar da kisan sojojin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar Ya ce sojojin sun rasu ne a yayin da suka kai ɗauki wurin da ake wani rikicin ƙabilanci a Ƙaramar Hukumar Bomadi ta Jihar Delta. Rundunar tsaron Nijeriyar ta tabbatar da cewa an kashe kwamanda ɗaya da sojoji biyu masu muƙamin manjo da kyaftin ɗaya da kuma kuratan sojoji 12. Birgediya Janar Tukur Gusau ya ce sojojin sun rasu a lokacin da suka yi ƙokarin kwantar da wata tarzoma da ta ɓarke tsakanin ƴan ƙabilar Okuama da Okoloba a ranar Alhamis. "Wasu matasa ne suka kewaye sojojin ranar Alhamis 14 ga watan Maris sannan suka kashe su," in ji kakakin hedkwatar tsaron ta Nijeriya. Sanarwar ta ce Shugaban Sojojin Nijeriya Christopher Musa ya bayar da umarni a gudanar da cikakken bincike kan mutuwar sojojin.