Rundunar sojin Nijeriya ta fitar da jerin hotunan jami'anta da aka yi wa kisan gilla a jihar Delta da ke kudancin ƙasar a makon da ya wuce. Rundunar sojin Nijeriya ta fitar da jerin hotunan jami'anta da aka yi wa kisan gilla a jihar Delta da ke kudancin Nijeriya a makon da ya wuce. Ta wallafa hotunan nasu ne a shafinta na X a yau Litinin da maraice, inda ta sake bayyana jimamin rashin da ta yi, wanda take zargin wasu ɓata-gari da aikata shi. Sanarwar rundunar na zuwa ne a daidai lokacin da take zargin al'ummar yankin da abin ya faru da hannu a kitsa lamarin, tare da yada farfaganda don "rufe aika-aikar da suka yi. Wannan lamari ya faru ne a a ranar Alhamis, lokacin da sojojin suka kai ɗauki a wani rikicin ƙabilanci da ke faruwa tsakanin al'ummomi biyu na yankin. Gwamnatin Nijeriya da ma al'ummar ƙasar da dama sun yi Allah wadai da "wannan ta'addanci", inda har Shugaba Bola Tinubu ya bai wa rundunar tsaro ƙasar "cikakken iko" na hukunta duk wanda aka samu da laifin kisan sojojin 17. Yaɗa farfaganda A sanarwar da ta fitar tun da fari a ranar Litinin da rana, rundunar sojin Nijeriya ta ce duk da mummunan kisan gillar da aka yi wa dakarunta a yankin, amma "abin takaicin shi ne yadda al'ummar wajen take amfani da kakafen watsa labarai wajen yaɗa farfagandar neman kare kansu, maimakon su taimaka wajen gano waɗanda suka aikata ɓarnar." "Wannan kuma wata alama ce da ke nuna cewa al'ummar yankin ce ta kitsa wannan hari na kisan da aka yi wa sojojin," in ji rundunar. Al'ummar yankin sun yaɗa labarin cewa sun ga mutane sanye da kakin soji suna ƙona gidaje a yankin, kwanaki kaɗan bayan da "matasa suk kashe dakarun" waɗanda aka aika su don magance wani rikici da ake yi a kan wajen zama. Amma runudnar ta yi kira ga ƴan Nijeriya da su yi watsi da labaran da al'ummar yankin ke yaɗawa, tana mai cewa suna yin hakan ne don neman kare kansu. "Wadannan sojoji ne da suka jajirce wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa da ma wadanda ba ‘yan kasa ba a yankin Neja-Delta, wadanda wasu gungun matasa masu dauke da makamai na al’ummar Okuama suka yi wa kisan gilla, ta hanyar rashin tausayi da imani, sannan suka wulaƙanta gawarwakinsu inda har suka fasa ƙirajensu suka ciro zuciyoyinsu, a matsayinsu na mutanen da aka tura dakarun don su ba su kariya," rundunar ta koka.
Taskar labarai
Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.
Rundunar sojin Nijeriya ta fitar da hotunan dakarunta da aka kashe a Delta
Rundunar sojin Nijeriya ta fitar da jerin hotunan jami'anta da aka yi wa kisan gilla a jihar Delta da ke kudancin ƙasar a makon da ya wuce. Rundunar sojin Nijeriya ta fitar da jerin hotunan jami'anta da aka yi wa kisan gilla a jihar Delta da ke kudancin Nijeriya a makon da ya wuce. Ta wallafa hot...

A taƙaice
Rundunar sojin Nijeriya ta fitar da jerin hotunan jami'anta da aka yi wa kisan gilla a jihar Delta da ke kudancin ƙasar a makon da ya wuce. Rundunar sojin Nijeriya ta fitar da jerin hotunan jami'anta da aka yi wa kisan gilla a jihar Delta da ke kudancin Nijeriya a makon da ya wuce. Ta wallafa hot...
