Manjo Janar Abdussalam ya jaddada cewa babu "wata farfaganda da bi-ta-da-ƙulli da ƙarairayi da za su janye hankalin dakarun daga cim ma manufofin da suka sanya a gaba". Rundunar sojojin ƙasa ta Nijeriya ta ce dakarunta ba za su fice daga yankin na Jihar Delta ba sai an "gano" mutanen da suka yi wa jami'anta goma sha bakwai kisan gilla a makon jiya. Kwamandan Runduna ta Shida da ke ƙarƙashin rundunar ko-ta-kwana a Kudu Maso Kudancin Nijeriya, Manjo Janar Jamal Abdussalam ne ya bayyana haka ranar Alhamis lokacin da shugaban hukumar raya yankin Neja-Delta Samuel Ogbuku ya ziyarce a Fatakwal. Sanarwar da rundunar sojin ta Nijeriya ta fitar ta ambato Manjo Janar Abdussalam yana cewa Hafsan Sojin Ƙasa na Nijeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya ba su umarnin "gano makaman da waɗanda suka aikata wannan ɗanyen-aiki suka ƙwace tare da tabbatar da ganin an kama dukkan masu hannu a lamarin." OKUAMA KILLING: WE WILL BE FIRM, STRONG, DECISIVE AND PROFESSIONAL IN OUR OPERATIONS, GOC ASSURES AS HE PLAYED HOST TO MD NDDC The General Officer Commanding, 6 Division, Nigerian Army/Land Component Commander, Joint Task Force, South South, Operation DELTA STATE, Major General… pic.twitter.com/6qGdTrKE9w — Nigerian Army (@HQNigerianArmy) March 21, 2024 Ya ƙara da cewa dakarunsu za su "ci gaba da zama a surƙuƙin (yankin Neja-Delta) har sai an cim ma waɗannan manufofi." Manjo Janar Abdussalam ya jaddada cewa babu "wata farfaganda da bi-ta-da-ƙulli da ƙarairayi da za su janye hankalin dakarun daga cim ma manufofin da suka sanya a gaba". Tinubu ya bai wa hedkwatar tsaron Nijeriya 'cikakken iko' na hukunta mutanen da suka kashe sojoji a Delta A ranar Alhamis ɗin makon jiya ne wasu ɓata-gari a ƙauyen Okuama na Jihar Delta suka kashe sojojin Nijeriya goma sha bakwai lokacin da suka je ƙauyen domin kai wa mutane ɗauki sakamakon rikicin ƙabilanci. Sojojin sun haɗa da kwamanda ɗaya da masu muƙamin manjo guda biyu da kyaftin ɗaya da kuma ƙananan sojoji 13. Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya bayyana matuƙar ɓacin ransa kan lamarin waɗanda ya ce ce "matsorata" ne suka aikata shi, yana mai bai wa Hedkwatar Tsaro da shugaban rundunar tsaron Nijeriya "cikakken iko" su hukunta duk wanda aka samu da laifi da hannu a kisan. Kazalika ya ce nan ba da jimawa ba za a yi wa sojojin jana'izar ban-girma tare da karrama su da lambobin yabo na ƙasa.
Haber arşivi
Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.
Rundunar sojin Nijeriya ta ce za ta ci gaba da zama a yankin Okuama sai ta gano mutanen da suka kashe jami'anta 17
Manjo Janar Abdussalam ya jaddada cewa babu "wata farfaganda da bi-ta-da-ƙulli da ƙarairayi da za su janye hankalin dakarun daga cim ma manufofin da suka sanya a gaba". Rundunar sojojin ƙasa ta Nijeriya ta ce dakarunta ba za su fice daga yankin na Jihar Delta ba sai an "gano" mutanen da suka yi w...

Bu haberde ne var?
Manjo Janar Abdussalam ya jaddada cewa babu "wata farfaganda da bi-ta-da-ƙulli da ƙarairayi da za su janye hankalin dakarun daga cim ma manufofin da suka sanya a gaba". Rundunar sojojin ƙasa ta Nijeriya ta ce dakarunta ba za su fice daga yankin na Jihar Delta ba sai an "gano" mutanen da suka yi w...
