Home / News archive
News archive

This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.

Sojoji sun kuɓutar da mutum 86 daga hannun Boko Haram a Borno

Dakarun Operation Hadin Kai sun daƙile harin ‘yan ta’adda tare da lalata sansaninsu Rundunar Operation Hadin Kai da ke yaƙi da ‘yan ta’addan Boko Haram a arewa maso gabashin Nijeriya ta ce ta kuɓutar da mutum 86 da aka yi garkuwa da su tare da daƙile wani hari da ‘yan ta’addan suka shirya a Jihar...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Updated 13/08/2026, 05:26:19
Sojoji sun kuɓutar da mutum 86 daga hannun Boko Haram a Borno
At a glance

Dakarun Operation Hadin Kai sun daƙile harin ‘yan ta’adda tare da lalata sansaninsu Rundunar Operation Hadin Kai da ke yaƙi da ‘yan ta’addan Boko Haram a arewa maso gabashin Nijeriya ta ce ta kuɓutar da mutum 86 da aka yi garkuwa da su tare da daƙile wani hari da ‘yan ta’addan suka shirya a Jihar...

Dakarun Operation Hadin Kai sun daƙile harin ‘yan ta’adda tare da lalata sansaninsu Rundunar Operation Hadin Kai da ke yaƙi da ‘yan ta’addan Boko Haram a arewa maso gabashin Nijeriya ta ce ta kuɓutar da mutum 86 da aka yi garkuwa da su tare da daƙile wani hari da ‘yan ta’addan suka shirya a Jihar Borno. A wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar Lahadi, ta ce lamarin ya faru ne ranar 9 ga watan Nuwamba bayan dakarun sun samu bayanan sirri cewa mayaƙan Boko Haram na kama mutane da motocinsu a kan hanyar Buratai zuwa Kamuya. Sanarwar ta ce bayan samun wannan bayani, dakarun Operation Hadin Kai suka kai farmaki a yankin Mangari, lamarin da ya sa ‘yan ta’addan suka tsere cikin firgici. Mai magana da yawun rundunar, Sani Uba, ya ce binciken da aka gudanar a yankin ya gano matsugunan wucin-gadi na ‘yan ta’addan inda aka kuɓutar da mutum 86 da aka yi garkuwa da su, ciki har da maza da mata da kuma ƙananan yara. Ya ƙara da cewa an ƙwace makamai da kayayyaki da suka haɗa da bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya, gidajen harsasai biyar da harsasai 73, da bindigogi huɗu, tare da motocin fararen hula biyar, babura biyar da kuma babura masu ƙafa uku guda biyu. Sanarwar ta kuma bayyana cewa sojojin sun lalata sansanin ‘yan ta’addan a yayin aikin. A wani samame na daban, dakarun da aka tura yankin Mangada sun kama mutum 29 da ake zargi da taimaka wa ‘yan ta’adda da kayayyakin amfani na yau da kullum a hanyarsu ta zuwa Chilaria. Kayayyakin da aka ƙwace daga hannunsu sun haɗa da a-kori-kura biyu, babur mai ƙafa uku ɗaya ɗauke da man fetur kimanin lita 1,000 a cikin jarka, galan huɗu na baƙin mai, sabbin tayoyin mota, magunguna da kuma abinci mai yawa. Rundunar ta ce an kammala aikin ba tare da wani soja ya ji rauni ba, lamarin da ya sa manyan sojoji suka yaba da bajintar da dakarun Operation Hadin Kai ke nunawa wajen yaƙi da ‘yan ta’adda a arewa maso gabashin Nijeriya. Tushen labari: Newstimehub