Shugaba Tinubu ya bai wa hedkwatar tsaro da shugaban rundunar tsaron Nijeriya "cikakken iko" na hukunta duk wanda aka samu da laifin kisan sojojin. Rundunar sojojin ƙasa ta Nijeriya ta fitar da hotunan wasu mutane da take nema ruwa-a-jallo bisa zargin kisan dakarunta goma sha bakwai a jihar Delta da ke kudancin ƙasar. Rundunar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, kwana guda bayan an yi wa sojojin jana'izar ban-girma a Abuja, babban birnin ƙasar. WANTED PERSONS IN CONNECTION TO THE KILLING OF 17 NIGERIAN ARMY PERSONNEL AT OKUAMA COMMUNITY pic.twitter.com/uFWkoYbKhe — Nigerian Army (@HQNigerianArmy) March 28, 2024 Mutanen takwas, ciki har da mace, su ne Akevwru Daniel Omotegbono wanda aka fi sani da suna Amagbem; Prof. Ekpekpo Arthur, Andaowei Dennis Bakriri da Igoli Ebi. Sauran su ne Akata Malawa David, Sinclair Oliki, Clement Ikolo Oghenerukevwe da kuma Reuben Baru. Hotunan jana'izar sojojin Nijeriya da aka kashe a jihar Delta Kusan mako biyu kenan Shugaba Tinubu ya bai wa hedkwatar tsaro da shugaban rundunar tsaron Nijeriya "cikakken iko" na hukunta duk wanda aka samu da laifin kisan sojojin.
Архив новостей
В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.
Rundunar sojin Nijeriya na neman mutum takwas ruwa-a-jallo kan kisan dakarunta a Delta
Shugaba Tinubu ya bai wa hedkwatar tsaro da shugaban rundunar tsaron Nijeriya "cikakken iko" na hukunta duk wanda aka samu da laifin kisan sojojin. Rundunar sojojin ƙasa ta Nijeriya ta fitar da hotunan wasu mutane da take nema ruwa-a-jallo bisa zargin kisan dakarunta goma sha bakwai a jihar Delta...

Кратко