Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

Ronaldo ya sa wa Mbappe albarka kan zuwansa Real Madrid

Cristiano Ronaldo ya aika saƙon fatan alheri ga Kylian Mbappe, wanda ya koma Real Madrid daga PSG. A ƙarshe dai, tauraron ɗan wasan nan ɗan asalin Faransa, Kylian Mbappe ya koma Real Madrid ta Sifaniya. An kwashe watanni ana raɗe-raɗin zuwansa Madrid, amma sai a wannan makon ne ya tabbatar da zuw...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:19
Ronaldo ya sa wa Mbappe albarka kan zuwansa Real Madrid
A taƙaice

Cristiano Ronaldo ya aika saƙon fatan alheri ga Kylian Mbappe, wanda ya koma Real Madrid daga PSG. A ƙarshe dai, tauraron ɗan wasan nan ɗan asalin Faransa, Kylian Mbappe ya koma Real Madrid ta Sifaniya. An kwashe watanni ana raɗe-raɗin zuwansa Madrid, amma sai a wannan makon ne ya tabbatar da zuw...

Cristiano Ronaldo ya aika saƙon fatan alheri ga Kylian Mbappe, wanda ya koma Real Madrid daga PSG. A ƙarshe dai, tauraron ɗan wasan nan ɗan asalin Faransa, Kylian Mbappe ya koma Real Madrid ta Sifaniya. An kwashe watanni ana raɗe-raɗin zuwansa Madrid, amma sai a wannan makon ne ya tabbatar da zuwansa Madrid. Bayan jin wannan labari ne tsohon gwarzon ɗan wasan Madrid, wanda a yanzu yake buga wa Al Nassr ta Saudiyya wasa, Cristiano Ronaldo ya aika wa Mbappe saƙon fatan alheri. Tun asali dai, Mbappe ya ɗauki Ronaldo a matsayin abin koyinsa tun yana ƙaramin yaro mai sha'awar ƙwallo. Haka nan Mbappe bai ɓoye burinsa na son taka leda a Real Madrid ba. Bayan kawo ƙarshen kwantiraginsa a PSG ta Faransa, Mbappe ya koma Madrid a Litinin ɗin nan, a hukumance. Mbappe ya wallafa wani hoto a shafinsa na Instagram, inda ya nuna shi yana ƙarami sanye da rigar Madrid, da kuma hoton gwaninsa Ronaldo a bayansa. Daga nan ne Ronaldo ya amsa masa inda ya aika masa saƙon fata na gari. Ronaldo ya yi tsokaci da cewa "Yanzu zan yi [kallo]. Ina farin cikin ganin ka haskaka Bernabeu. #HalaMadrid". Saƙon ya faranta wa dubban masoyan Madrid a faɗin duniya. Masoyan na Madrid za su yi fatan ganin Mbappe ya bi sahun Ronaldo a Madrid, wanda ya ci ƙwallaye 450 da tallafin ƙwallo 131 a wasanni 438 da ya buga wa Madrid, kuma ya ci kofuna 16 a shekaru tara, da kyautar gwarzon duniya sau biyar. Sai dai a yanzu Mbappe zai fara atisaye ne da tawagar ƙasar Faransa, gabanin fara gasar cin kofin ƙasashen Turai da za a yi a Jamus. Ba zai buga wa Madrid wasa ba, sai an zo wasannin sharar fage inda za su kai ziyara Amurka.