Ronaldo ya ci kwallonsa ta 50 a bana a lokacin da kungiyar Al Nassr take fafatawa da Al Shabab inda aka tashi 5-2 a Gasar Cin Kofin Sarkin Saudiyya. Christiano Ronaldo ya ce har yanzu akwai sauran kwallayen da zai ci a bana bayan ya ci kwallonsa ta 50 a 2023. Ya bayyana haka ne bayan kungiyarsa ta Al Nassr ta ci Al Shabab 5-2 a gasar Cin Kofin Sarkin Saudiyya. Tsohon dan wasan na Manchester United da Real Madrid ya ci kwallon a kusa da kusa da kafarsa ta dama a minti na 74. “Babban nasara kuma ina farin cikin sanar da cin kwallota ta 50 a 2023,” kamar yadda dan wasan na Portugal mai shekara 38 ya rubuta a shafinsa na Instagram bayan kwallon tasa ta taimaka wa kulob din ya kai zagayen kusa da na karshe a ranar Litinin. “Ina godiya da irin goyon bayan da na samu daga ‘yan kungiyata da magoya bayana da kuma iyalina! Akwai sauran damar cin wasu a bana.” Dan wasan ya ci akalla kwallo daya a kusan duka wasan da ya buga wa kungiyar ta Al Nassr. Haka kuma ya ci kwallon goma ga Portugal a wasanni tara da ya buga a 2023.
أرشيف الأخبار
يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.
Ronaldo ya ce yana sa ran cin karin kwallaye a 2023
Ronaldo ya ci kwallonsa ta 50 a bana a lokacin da kungiyar Al Nassr take fafatawa da Al Shabab inda aka tashi 5-2 a Gasar Cin Kofin Sarkin Saudiyya. Christiano Ronaldo ya ce har yanzu akwai sauran kwallayen da zai ci a bana bayan ya ci kwallonsa ta 50 a 2023. Ya bayyana haka ne bayan kungiyarsa t...

لمحة سريعة