Accueil / Archives
Archives

Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.

Rodri da Ederson sun warke, za su buga wa Manchester City wasansu da Tottenham - in ji Pep Guardiola

Kocin Man CIty, Guardiola ya ce har yau ‘Rodri shi ne gwarzon ƙwallo na duniya”, yana mai cewa ɗan wasan zai buga musu wasan nasu na gaba da Spurs ran Asabar mai zuwa. Yayin da Manchester City ta buga wasanta na farko a kakar gasar Firimiya ta bana tare da Wolves, golanta Ederson da tauraron ɗan...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Mis à jour 13/08/2026 05:26:19
Rodri da Ederson sun warke, za su buga wa Manchester City wasansu da Tottenham - in ji Pep Guardiola
En bref

Kocin Man CIty, Guardiola ya ce har yau ‘Rodri shi ne gwarzon ƙwallo na duniya”, yana mai cewa ɗan wasan zai buga musu wasan nasu na gaba da Spurs ran Asabar mai zuwa. Yayin da Manchester City ta buga wasanta na farko a kakar gasar Firimiya ta bana tare da Wolves, golanta Ederson da tauraron ɗan...

Kocin Man CIty, Guardiola ya ce har yau ‘Rodri shi ne gwarzon ƙwallo na duniya”, yana mai cewa ɗan wasan zai buga musu wasan nasu na gaba da Spurs ran Asabar mai zuwa. Yayin da Manchester City ta buga wasanta na farko a kakar gasar Firimiya ta bana tare da Wolves, golanta Ederson da tauraron ɗan wasanta Rodri ba su samu halartan wasan ba. Ederson ɗan asalin Brazil ya yi fama da ciwon ciki, inda madadinsa, James Trafford ya yi ƙoƙari sosai kuma ba a ci shi ba a wasan da suka doke Wolves da ci 4-0. A baya an yi tararrabi kan makomar Ederson a tawagar City, musamman bayan zuwan Trafford, wanda ɗan makarantar koyar da ƙwallo ta Man City ne, wanda ya dawo ƙungiyar bayan kwashe shekaru biyu a Burnley. Mai shekaru 32, Ederson ya samu tayi daga manyan ƙungiyoyi kamar Galatasaray, amma a yanzu zai yi fatan samun gurbi a tawagar koci Pep Guardiola don ganin bai bar shi yana ɗumama benci ba. Wasan City na gaba tare da Tottenham yana da ban tsoro saboda City ta sha kashi a hannunsu sau tara a duka gasanni, kuma idan ban da Liverpool babu wanda ya taɓa doke su da yawa haka. Rodri gwarzon duniya