Accueil / Archives
Archives

Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.

Rikicin Masarautar Kano: An tura ƙarin 'yan sanda Fadar Sarki ta Ƙofar Kudu da Gidan Nasarawa

Kwamishinan 'yan sandan jihar mai barin gado Usaini Gumel ne ya bayyana haka a hira da manema labarai ranar Litinin a birnin Kano. Rundunar 'yan sandan Nijeriya reshen Jihar Kano ta ce ta tura ƙarin jami'ai a fadar Sarki na 14 Muhammadu Sanusi na II da ke Ƙofar Kudu da kuma Gidan Nasarawa, inda S...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Mis à jour 13/08/2026 05:26:19
Rikicin Masarautar Kano: An tura ƙarin 'yan sanda Fadar Sarki ta Ƙofar Kudu da Gidan Nasarawa
En bref

Kwamishinan 'yan sandan jihar mai barin gado Usaini Gumel ne ya bayyana haka a hira da manema labarai ranar Litinin a birnin Kano. Rundunar 'yan sandan Nijeriya reshen Jihar Kano ta ce ta tura ƙarin jami'ai a fadar Sarki na 14 Muhammadu Sanusi na II da ke Ƙofar Kudu da kuma Gidan Nasarawa, inda S...

Kwamishinan 'yan sandan jihar mai barin gado Usaini Gumel ne ya bayyana haka a hira da manema labarai ranar Litinin a birnin Kano. Rundunar 'yan sandan Nijeriya reshen Jihar Kano ta ce ta tura ƙarin jami'ai a fadar Sarki na 14 Muhammadu Sanusi na II da ke Ƙofar Kudu da kuma Gidan Nasarawa, inda Sarki na 15 Aminu Ado Bayero yake da zama. Kwamishinan 'yan sandan jihar mai barin gado Usaini Gumel ne ya bayyana haka a hira da manema labarai ranar Litinin a birnin Kano. Ya ƙara da cewa sun ɗauki matakin ne "domin daƙile duk wata barazana da ka iya tasowa a waɗannan wurare.” Dambarwar da ake yi a Kano kan Sarauta “An tura ƙarin jami'an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a Fadar Ƙofar Kudu, gidan Sarki Malam Muhammadu Sanusi, da kuma ƙaramar fada ta Nasarawa, inda Sarki Aminu Bayero yake da zama,” in ji shi. Kwamishina Gumel ya yi kira ga mazauna birnin na Kano su ci gaba da bai wa 'yan sanda haɗin kai ta hanyar ba su duk wani labari da zai tabbatar da tsaron jihar.